TURKIYYA
2 minti karatu
Turkiyya, Masar sun haɗa kai don magance rikicin yankinsu, sun yi watsi da shirin sake mamaye Gaza
Ƙasashen biyu sun sha alwashin haɗa gwiwa a yunƙurin shawo kan ƙalubalen da yankin Gabas ta Tsakiya yake fama da shi, a cewar Ministan Harkokin Wajen Masar.
Turkiyya, Masar sun haɗa kai don magance rikicin yankinsu, sun yi watsi da shirin sake mamaye Gaza
Masar da Turkiyya sun sha alwashin yin cinikayya da ta kai $15B a wannan shekarar, tare da gudanar da taruka masu muhimmanci / AA
9 Agusta 2025

Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdelatty ya sanar ranar Asabar cewa suna haɗa gwiwa da Tukiyya a hanyoyin warware rikice-rikicen da ke addabar yankin, bayan ganawar da ya yi da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan a El Alamein, Masar.

A wani taron manema labarai na haɗin gwiwa, Abdelatty ya bayyana halin da ake ciki a dangantakar Masar da Turkiyya a matsayin “muhimmin mataki na alaƙa mai ƙarfi.”

Ministocin biyu sun tabbatar da “amincewa da yunƙurin haɗa kai tare da yin amfani da dukkan dama wajen tunkarar shirin Isra’ila na mamaya da kuma tasirinsa,” in ji shi.

Taron gaggawa na OIC

Fidan ya ce Turkiyya za ta kira taron gaggawa na Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmai wato Organization of Islamic Cooperation (OIC) domin tattauna shirin Isra’ila na cikakkiyar mamaya a Gaza.

"(Game da shirin Isra’ila a kan Gaza) A matsayina na shugaban Ƙungiyar Ministocin Ƙasashen Waje na ƙasashen (OIC), mun yanke shawarar kiran taron ƙungiyar OIC," in ji Fidan a taron manema labarai.

Kazalika Fidan ya soki manufar Isra’ila, yana mai cewa: "Mun yi watsi baki ɗaya da aniyar (Isra'ila) ta cikakkiyar mamaya a Gaza; Wannan shiri sabon babi ne na mamayar Isra'ila da yaƙin da take yi na kisan ƙare-dangi."

Ya ƙara da cewa: “Turkiyya da Masar za su ci gaba da ƙin amincewa da wannan shiri.”

Da yake magana game da ayyukansu na jinƙai, Fidan ya ce: "Kawo yanzu mun turo aƙalla tan 102,000 na kayan agaji ga ‘yan’uwanmu da ke Gaza. Muna godiya ga Masar bisa haɗin kanta wajen isar da waɗannan kayan agaji."

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us