Jumullar mutum 246,228 ne da kuma gidaje 32,251 ambaliyar ruwa ta shafa a Jamhuriyar Nijar sakamakon ruwan saman da aka fara tun daga farkon damina.
Kwamitin Kula da Bayar da Kariya ga Ambaliya a Nijar ne ya tabbatar da waɗannan alƙaluma a yayin taronsa na huɗu da aka gudanar a ranar Juma’a, 12 ga Satumbar 2025 a ɗakin taro na ofishin Firaminista.
A cewar kwamitin, zuwa yanzu, ambaliyar ta shafi unguwanni da ƙauyuka 1,009 a cikin ƙananan hukumomi 122, yayin da “tallafin da aka bayar zuwa 2 ga Satumbar 2025 ya kai ga gidaje 18,962 da suka ƙunshi mutum 142,642 tare da tan 1,896.2 na hatsi a cikin tallafin da aka bayar sau uku”.
“An bayar da umarni na musamman domin tabbatar da cewa tallafin ya kai ga waɗanda suke da bukatarsa,” in ji majiyar.
Kanal Manjo Salissou Mahaman Salissou wanda shi ne Ministan Ayyuka Da Ababen More Rayuwa kuma mataimakin wannan kwamitin shi ne ya jagoranci zaman kwamitin.
Ajandar taron ta mayar da hankali ne kan amincewa da bayanan taron da ya gabata, yanayin ambaliyar ruwa na yanzu da matakan da aka ɗauka, da kuma shirin shiga shekarar karatu ta 2025–2026.
“Dangane da bayanan da aka sabunta zuwa 10 ga Satumbar 2025, ana aiwatar da zagaye na 4 na tallafin domin kaiwa ga gidaje 9,976 da suka ƙunshi mutum 79,442,” in ji kwamitin.
Kwamitin ya kuma yi tsokaci kan tasirin wannan ambaliyar ruwa ga gine-ginen makarantu.
“Dangane da gine-ginen makarantu da ambaliyar ta shafa, ana buƙatar sake gina aƙalla ajujuwa 524, banɗakunan makarantu 511 da sassan gudanarwa na makarantu 157. Haka kuma dole a fice daga makarantu 238 da ke da jumullar ajujuwa 271 waɗanda ambaliyar ta shafa kafin shiga sabon zangon karatu,” in ji kwamitin.