AFIRKA
2 minti karatu
Sudan ta yi maraba da ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙi da RSF, ta yi watsi da katsalandan na ƙasashen waje
Wannan na zuwa ne bayan wata sanarwar haɗin gwiwa da Masar da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, da Amurka suka fitar inda suka yi kira da tsagaita wuta domin barin kayan agaji shiga sassan Sudan.
Sudan ta yi maraba da ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙi da RSF, ta yi watsi da katsalandan na ƙasashen waje
Fiye da mutum 20,000 sun mutu kuma an raba mutum miliyan 15 da muhallansu, a cewar alƙaluman Majalisar Dinkin Duniya da na cikin gida. / Reuters
15 awanni baya

Sudan ta yi maraba da kokarin kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a ƙasar da kuma hare-haren da dakarun Rapid Support Forces (RSF) ke kaiwa, tana mai jaddada kin amincewa da duk wani shisshigi daga ƙasashen waje cikin harkokin cikin gida na ƙasar.

“Gwamnatin Sudan tana maraba da duk wani yunƙuri na yankin ko na ƙasa da ƙasa da zai taimaka wajen kawo ƙarshen yaƙin, dakatar da hare-haren ta’addanci na dakarun RSF kan birane da kayayyakin more rayuwa, da kuma cire takunkumin da aka sanya wa birane domin kada a sake maimaita bala’o’i da laifukan da aka aikata wa al’ummar Sudan,” in ji Ma’aikatar Harkokin Waje a wata sanarwa da ta wallafa a X ranar Asabar.

Sanarwar ta biyo bayan wata sanarwar haɗin gwiwa daga Masar, Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Amurka, inda suka buƙaci a samu “tsagaita wuta ta jin kai” a Sudan domin ba da damar shigar kayan agaji cikin sauri zuwa dukkan sassan ƙasar.

Fadan El-Fasher

Ma’aikatar ta sake jaddada kin amincewa da duk wani “shisshigi na ƙasa da ƙasa ko na yankin da ba ya mutunta ikon mulkin Sudan, cibiyoyin ta na doka, da kuma hakkinta na kare mutanenta da kasarta.”

Ta nuna baƙin ciki kan gazawar al’ummar duniya wajen tilasta wa RSF “ta aiwatar da ƙudurorin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya 2736 da 1591, ta cire takunkumin da aka sanya wa birnin El-Fasher, ta rage wahalhalun da jama’arsa ke fuskanta, ciki har da tsofaffi, mata, da yara, da kuma ba da damar wucewar motocin agaji.”

El-Fasher ta sha fama da mummunan faɗa tsakanin sojojin Sudan da RSF tun watan Mayun 2024, duk da gargaɗin ƙasa da ƙasa kan haɗarin tashin hankali a birnin da ke zama cibiyar jin ƙai mai muhimmanci ga jihohin Darfur guda biyar.

RSF da sojojin Sudan suna cikin rikici mai tsanani na neman iko tun watan Afrilun 2023, wanda ya haifar da mutuwar dubban mutane da kuma jefa Sudan cikin ɗaya daga cikin mafi munin rikicin jin ƙai a duniya.

Fiye da mutum 20,000 sun mutu kuma an raba mutum miliyan 15 da muhallansu, a cewar alƙaluman Majalisar Dinkin Duniya da na cikin gida.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us