AFIRKA
2 minti karatu
Rundunar Sojin Ghana za ta yi cikakken bincike kan hatsarin helikwafta – Mahama
Shugaban ƙasar ya ce za a yi wa waɗanda suka mutu a hatsarin jana’iza ta ƙasa.
Rundunar Sojin Ghana za ta yi cikakken bincike kan hatsarin helikwafta – Mahama
Shugaban John Dramani Mahama ya yi jawabi ga 'yan ƙasar karin farko bayan aukuwar hatsarin da ya kashe ministoci biyu da wasu jami'an gwamnatin ƙasar / Getty
8 Agusta 2025

Shugaba John Mahama ya tattabar wa mutanen ƙasarsa cewa rundunar sojin ƙasar za ta gudanar da cikakken bincike kan abin da ya janyo hatsarin helikwaftan da ya kashe ministoci biyu da wasu jami’a gwamnatin Ghana. 

Da yake jawabinsa na farko tun bayan hatsarin a fadar gwamnatin ƙasar ranar Alhamis, Shugaba Mahama ya bayyana alhininsa tare da miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su

Ya ce duk da cewa al’umar ƙasar na son sanin abin da ya janyo hatsarin, ya kamata ‘yan ƙasar su haɗa kai a wannan lokacin makokin. 

“Yayin da muke juyayi, dole mutane za su yi ta tambaya game da silar wannan bala’in kuma [tambayoyin] na da muhimmanci.,” in ji shi.

Shugaba Mahama ya jaddada jajircewar gwamnatin wajen gano gaskiyar abin da ya janyo hatsarin, yana mai tabbatar wa ‘yan ƙasar Ghana cewa babu wani bayanin da za a ɓoye musu. 

Jaridun ƙasar sun ambato Shugaba mahama yana cewa: “Ina son in tabbatar wa iyalai da ƙasar cewa Rundunar Sojin Ghana ta fara cikakken bincike game da yanayin da wannan hatsarin ya auku.”

Kalaman shugaban ƙasar na zuwa ne yayin da ƙasar ta fara zaman makoki na kwanaki uku domin martaba wadanda suka mutu a hatsarin. 

Ana tsammanin ‘yan ƙasar su gabatar da furanni na girmamawa tare da kunna kyadir daga ranar Alhamis zuwa ranar Asabar inda za a gama zaman makokin a wani zaman tunawa da mamatan a fadar gwamnatin ƙasar da yammacin ranar 9 ga watan Agusta.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us