NIJERIYA
3 minti karatu
INEC na shirin bai wa fursunoni a Nijeriya damar zaɓe — Shugaban INEC
“Muna sane cewa ‘yancin kaɗa ƙuri’a ‘yancin ɗan’adam ne wanda ba za a iya hana ko wane ɗan ƙasa ba, ko don yana wani gidan gyra hali," in ji Farfesa Yakubu yayin da Shugaban Hukumar Gidajen Gyaran hali ta kasa Sylvester Nwakuche ya kai masa ziyara.
INEC na shirin bai wa fursunoni a Nijeriya damar zaɓe — Shugaban INEC
INEC / TRT Afrika Hausa
8 Agusta 2025

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) ta ce tana aiki da hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali ta Nijeria (NCoS) kan bai wa fursunoni damar yin zaɓa. 

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakar ranar Juma’a yayin da yake karɓar baƙuncin Shugaban Hukumar Gidajen Gyaran hali ta Nijeriya, Sylvester Nwakuche, a hedikwatar hukumar da ke Abuja.

Yakubu ya ce ya amince da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ya bai wa fursunoni ‘yancin yin rijista da kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓuka.

“Muna sane cewa ‘yancin kaɗa ƙuri’a ‘yancin ɗan’adam ne wanda ba za a iya hana ko wane ɗan ƙasa ba, ko don yana wani gidan gyaran hali. A wurare da dama a duniya, ciki har da wasu ƙasashen Afirka irin su Ghana da Kenya da Afirka ta Kudu, fursunoni suna yin amfani da ‘yancinsu na kaɗa ƙuri’a,” in ji Yakubu.

“Kamar yadda ka sani, zaɓe wani tsari ne da ake aiwatarwa a bisa doka. Idan muka yi aiki tare, za mu iya yi amfani da damar garambawul da ake yi wa dokar zaɓe domin samun wani tanadi na doka wanda zai iya shafar ‘yan ƙasa da ke gidajen gyara hali,” in ji Yakubu.

‘Fursunoni suna da ‘yancin yin zaɓe’

Shugaban na INEC ya ce abin da ya dace su yi yanzu shi ne su nemi taimakon majalisun dokokin ƙasar domin samun ƙarin haske da kuma madogarar doka kan batun.

Tun da farko, Shugaban Hukumar ta Gyaran Hali ta Nijeriya Sylvester Ndidi Nwakuche Ofori ya ce ya je INEC ne domin neman bai wa fursunoni damar kaɗa ƙuri’a bisa tanade-tanden doka.

Ya bayyana cewa “akwai fiye da ‘yan Nijeriya 81,000 a gidajen gyaran hali a ƙasar - fiye da 66% masu jiran shari’a ne, don haka a ƙarƙashin doka ba masu laifi ba ne.”

Ya kamata mu yi taka-tsantsan da yadda ake mu’amala da su. Suna da ‘yanci, kuma ɗaya daga cikin ‘yancin da suke da shi shi ne ‘yancin kaɗa ƙuri’a. Kasancewar ana tsare da su bai kamata ya raba su da kasancewar su ‘yan ƙasa ba,” a cewar Sylvester.

Wata sanarwa da INEC ta fitar kan ziyara ta ce duk da ba sanya takamaimen lokaci ba, ganawar shugabannin na nuna alamar cewa baki ya zo ɗaya tsakanin INEC ha hukumar kula da gidajen gyaran hali cewa lokaci ya yi da Nijeriya za ta shiga cikin ƙasashen da suka bai wa fursunoni damar kaɗa ƙuri’a yayin zaɓuka.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us