Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da ƙwace mahaƙar zinari ɗaya tilo a ƙasar, bayan da ta zargi kamfanin Australia da ke gudanar da ita da "manyan laifukan keta doka" a yayin da gwamnatin take neman karɓe ragamar harkokin ma’adanai na ƙasar.
Gwamnatin soji, wadda ta ƙwace mulki daga gwamnatin farar-hula a shekarar 2023, ta sha alwashin magance rashin tsaro da ya addabi ƙsar.
Kamfanin McKinel Resources Limited na Australia ta amshi ragamar gudanar da haƙar zinari ta Societe des mines du Liptako (SML), wadda ke Kogin Neja a 2019 bayan ta sayi kaso mafi tsoka daga wurin gwamnati.
"Sakamakon manyan laifukan keta dokoki da kuma manufarmu ta ceto wannan kamfani mai matukar muhimmanci, gwamnatin Nijar ta yanke shawarar ƙwace kamfanin SML da mayar da shi na ƙasa," a cewar wata sanarwa da shugaban mulki soji, Janar Abdourahamane Tiani, wadda aka karanto a gidan tabijin na ƙasar ranar Juma’a da maraice.
"Wannan mataki ya yi daidai da manufar shugaban Jamhuriya ta miƙa dukkan ragamar tafiyar da albarkatun ƙasa na ƙasar ga hannun al’ummar Nijar," in ji sanarwar.