Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya ba da umarnin hanzarta ƙaddamar da shirin kiwon lafiya kyauta ga 'yan fansho marasa galihu a ƙasar.
Mashawarcin shugaba Tinubu kan ba da bayanai, Bayo Onanuga ne ya ba da wannan sanarwar yau, 6 ga Agusta 2025.
Shirin zai gudana ne ƙarƙashin Tsarin Karo-karon Fansho na ƙasa.
Umarnin da shugaban ya bayar ya kuma ƙunshi gaggauta ƙaddamar da ƙarin kuɗin fansho, da mafi ƙarancin fansho ga masu ritaya.
Shugaban ya ce ƙaddamar da shirin wani ɓangare ne na kyautata kariyar al’umma bayan sun yi ritaya.
Shugaban Ƙasar ya ba da wannan umarnin ne bayan ya gana da Shugabar Hukumar Fansho ta Ƙasa, Ms. Omolola Oloworaran.
Bugu da ƙari, shugaban ya umarci Ms Oloworaran ta gaggauta warware matsalar fanshon ‘yan sanda.
A nata jawabin, shugabar hukumar fanshon ta ce tana aiki don tabbatar da kare darajar kadarorin fansho daga lahanin hauhawar farashi da tarnaƙin tattalin arziƙi.
Ta kuma ce akwai shirin fara amfani da kuɗaɗen ƙasashen waje cikin kuɗin karo-karon ma’aikata, domin ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje su shiga tsarin fanshon zamani.