Kisan gillar da aka yi wa Sadiq Gentle, babban mai taimaka wa gwamnan Jihar Kano a Hukumar Tarihi da Al’adu ya ƙara fito da girman matsalar ƙwacen waya da harkar daba a jihar da ke arewacin Nijeriya.
Maharan, waɗanda wasu suke zargin masu ƙwacen waya ne amma gwamnati ta zargi ɓata-gari ne, sun kai wa marigayin farmaki har gida a ƙarshen makon jiya, ko da yake ya shafe ’yan kwanaki a asibiti har ma an yi wa Sadiq tiyata a wuraren da maharan suka caccaka masa makami, kafin rasuwarsa a ranar Alhamis.
Sannan idan za a tuna akwai wani ɗalibin Jami’ar Bayero mai suna Umar Abdullahi Hafizi da shi ma masu ƙwacen waya suka kashe a wannan mako a Kano.
Za a iya cewa matsalar ƙwacen waya da faɗace-faɗacen daba na ci gaba da ci wa al’umma Jihar Kano tuwo a ƙwarya, domin kuwa babu ranar da za ta zo ta wuce ba tare da an samu rahoton faɗan daba, ko na ƙwacen waya ba a sassan jihar daban-daban, abin da ke sanya fargaba da tsoro a zuƙatan al’ummar jihar.
Saboda tsananin yadda abin ya yi muni da yadda ake yawan samun faruwar matsalar, akwai hanyoyi da unguwannin Kano da jama’a suke ƙaurace musu musamman idan dare ya yi.
Ko da yake za a iya cewa matsalar ƙwacen waya da ayyukan ’yan daba ba ta taƙaita a Jihar Kano ba, saboda ko a watan Yunin da ya gabata wani soja ya rasa ransa a hannun wani mai ƙwacen waya a Jihar Kaduna, bayan da ɓarawon ya caka masa wuƙa a ƙirjinsa.
Mece ce mafita?
Wasu masana suna ganin cewa talauci da rashin aikin yi da rashin hukunta ɓarayin waya da ƙarancin tsaro suna cikin dalilan da suka sa matsalar ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa.
Ko da yake akwai wasu masana da suke ganin matsalar ƙwacen waya da faɗace-faɗacen daba alama ce ta wata babbar matsala kuma har sai an magance babbar matsalar kafin za a fara ganin haske.
Galibi masanan suna alakanta wannan matsala da yadda ake zamantakewar aure da yadda ake tarbiyyar yara waɗanda idan ba a kula da su ba yadda ya kamata, su ne suke girma su addabi al’umma.
Masu ilimin zamantakewa na ganin iyaye ne ya kamata su zama matakin farko na kawo gyara a cikin irin wannan lamari, saboda abu ne mai alaƙa da rushewar tarbiyya.
Sai dai sun koka kan yadda abin takaici a mafi yawan lokuta iyayen ba sa son laifin ‘ya’yansu ta yadda ko kama yaran aka yi da laifin, to su ne kan gaba wajen ganin ba a yi musu hukunci na shari’a ba balle har hakan ya yi tasiri.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce tana ɗaukar mataki don magance matsalar, ciki har da ƙaddamar da Operation Kukan Kura, wanda a cikin kwana 40 da kaddamar da shi aka kama fiye da mutum 500 bisa zargin daba da ƙwacen waya, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida wa TRT Afirka Hausa.
Masanin tsaro kuma tsohon kwamishinan ’yan sanda a Jihar Kano CP Muhammad Wakili mai ritaya (Singham) ya taba shaida wa TRT Afrika Hausa cewa kamen da jami’an tsaro suke yi wa masu ƙwacen waya ‘yan daba zai yi maganin matsalar ne na dan wani lokaci.
Kazalika masana zamantakewa na ganin akwai buƙatar shirya ganganmin wayar da kan iyaye da ma yaran baki ɗaya, na gyaran tarbiyya da yi wa zamantakewa gaba ɗayanta garanbawul idan har ana so a ga haske da gyara a cikin al’umma.
Babban abin da yake damun wasu masu bibiyar lamuran shi ne yadda jama’ar unguwannin da abin ya shafa suka kasa yin katabus.
Abin da kawai suke iya shi ne da zarar ‘yan daban sun iso sai kowa ya shige gida ya rufe, a bar yaran su ci karensu ba babbaka, idan tsautsayi ya fada kan ɗan ba-ruwana a ji masa rauni, gobe ma haka, jibi ma haka.
Girman lamarin ya kai har mata a unguwannin Zango da Korar Mata sun fita sun yi zanga-zanga saboda yadda ake neman hana su sakat su da yaransu.
Shin wai babu wani abu da jama’ar unguwannin da fadan daba ke addaba za su iya yi ne?
Ina masu hankalin unguwannin matasa majiya karfi? Ko su ma guduwa suke yi su shige gida a kulle tare da mata da ƙananan yara, yayin da ƙannensu ‘yan kasa da shekaru 25 suke abin da suka ga dama, sai sun gama sun tafi a fito a kafa dabar mayar da zance ana cewa ai har da wane dan gidan wane?
Ko da rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ta kaddamar da Kukan Kura, tana jinjina wa jama’ar da suka yi kukan kura suka yi wa kansu maganin matsalar, maimakon rige-rigen rufe kofofi ana lekowa ta tagogi.
Ku a ganinku, ta yaya za a iya kawo ƙarshen masu ƙwacen waya da dabanci?