NIJERIYA
2 minti karatu
An yi zanga-zanga a Zamfara kan sabbin hare-haren ‘yan bindiga
Wannan na zuwa ne kwanaki bayan wani malamin addini, Malam Yusuf Musa Asadussunah ya ce ɗan bindiga Bello Turji ya mika makamansa tare da sake wasu da ya yi garkuwa da su bayan gwamnatin Nijeriya ta yi sulhu da shi.
An yi zanga-zanga a Zamfara kan sabbin hare-haren ‘yan bindiga
Gwamna Dauda Lawal - Jihar Zamfara Najeriya / Others
8 Agusta 2025

Ɗaruruwan mutane, yawancinsu tsofaffin mata da masu goyo daga ƙauyen Jimrawa na ƙaramar hukumar Kaura Namoda na Zamfara, sun gudanar da zanga-zangar lumana ranar Alhamis a Gusau, babban birnin Jihar game da rashin tsaro a ƙauyensu.

Wannan na zuwa ne makonni biyu bayan mazauna ƙaramar hukumar Gusau ta jihar Zamfara suka yi zanga-zanga inda suka ce hare-haren ‘yan bindiga babu ƙaƙƙautawa sun kashe sama da mutum 100 a ƙauyukan da suka haɗa da Mada da Ruwan Bore da Fegin Baza da Lilo, da kuma Bangi.

Kaura Namoda da wasu ƙananan hukumomi a jihar Zamfara na fama da hare hare-haren ‘yan bindiga da suke kashe tare da garkuwa da gomman mutane inda suka lalata gidaje da dukiyoyin jama’a kuma suka raba mutane da muhallensu.

Jaridar Daily Trust ta Nijeriya ta ambato mazauna jihar na cewa rashin kyawun hanyoyin jihar na taimaka wa ɓarayin daji domin jami’an tsaro na fuskantar gagarumin ƙalubale wajen kai ga yankunan da lamarin ya shafa da wuri.

Sojojin Nijeriya sun tarwatsa bikin 'yan ta'adda, sun kashe 30 a jihar Zamfara

Masu zanga-zangar daga ƙauyen Jimrawa sun kutsa cikin fadar gwamnatin jihar da ke Gusa inda suƙa nemi jami’an tsaro su kai musu ɗauki.

Jimrawa ɗaya ne daga cikin mazaɓu shida inda za a yi zaɓen cika gurbi na ranar 16 ga watan Agusta, a cewar hukumar zaɓe ta Nijeriya (INEC).

Sai dai kuma, taɓarɓarewar tsaro a yankin na hana mutane rayuwa kamar yadda aka saba, inda rahotanni suka ce mazauna garin da yawa na hannun ‘yan bindiga.

Masu zanga-zangar sun nemi gwamnan jihar Dauda Lawal, ya cika musu alƙawarin da ya yi musu a lokacin yaƙin neman zaɓe wajen tabbatar da tsaro a ƙauyensu nasu.

Wannan na zuwa ne kwanaki bayan wani malamin addini, Malam Yusuf Musa Asadussunah ya ce ɗan bindiga Bello Turji ya mika makamansa tare da sake wasu da ya yi garkuwa da su bayan gwamnatin Nijeriya ta yi sulhu da shi.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us