Daga Gabriella Waaijman
A matsayina na mai aikin jinƙai, ina samun ƙwarin gwiwar cewa aikina yana kawo sauyi mai ma’ana ga rayuwar miliyoyin yara.
Ƙa’idar cewa dukkan rayukan bil’adama suna da daraja iri ɗaya ita ce ke ƙarfafa ni da sauran ma’aikatan agaji, ko da kuwa a cikin mawuyacin yanayi.
Amma a yau, muna fuskantar wata matsala mai tsanani fiye da yadda muka taɓa zato: gaskiyar da ba za a iya jurewa ba ta zaɓar waɗanne rayuka za a ceta kuma waɗanne za a bari.
Wannan wata masifa ce da ba za mu iya da ita ba — kuma bai kamata mu amince da ita ba.
Rage tallafin ƙasashen waje da aka yi a baya bayan nan yana tilasta wa ƙungiyoyin jinƙai yanke shawarwari masu wahala.
A lokacin da ɗaya cikin yara 11 a duniya ke buƙatar taimakon jinƙai, muna tilasta wa fifita wata matsala a kan wata, wata al’umma a kan wata, kuma a ƙarshe, rayuwar wani yaro a kan ta wani.
Tuni mun riga mun yanke shawarwari masu raɗaɗi na dakatar da shirye-shiryen ceton rayuka.
Wato ina nufin kamar kula da lafiyar yara masu fama da matsananciyar tamowa da yunwa ko kuma kulawar lafiya mai muhimmanci ga jarirai a wuraren yaƙi.
Wannan ba kawai ƙalubale ne na dabaru ba; matsala ce ta ɗabi’a da ke taɓa zuciyar aikinmu da ruhinmu, da duk abin da muke tsayawa a kai.
Ka’idoji na cikin haɗari
An kafa Ƙungiyar Save the Children fiye da ƙarni guda da ya wuce ta hannun Eglantyne Jebb, wata mace mai ƙarfin zuciya da ƙuduri.
Ta kafa wata ƙungiya da aka sadaukar don kare haƙƙin yara da ceton rayuka da kare iyalai da rage wahala, da dawo da mutunci.
A yau, muna aiki a ƙasashe 115, muna tallafa wa yara sama da miliyan 105 kai tsaye kowace shekara.
Muna yawan kasancewa cikin farkon masu amsa kiran gaggawa, kuma sadaukarwarmu ga kowane yaro, a ko ina, ba ta da sassauci.
Duk da haka, ka’idojinmu suna cikin barazana mai tsanani.
A wani zamani na ƙara yawaitar matsalolin duniya—rikici da sauyin yanayi, da matsalar tattalin arziki—yawancin ƙasashen duniya masu arziki suna rage kasafin kuɗin tallafinsu.
Amurka da Birtaniya da Jamus da Ostiraliya da Sweden da Denmark da Faransa da Netherlands da sauran ƙasashen da ke bayar da tallafi na gargajiya suna ja da baya daga alkawuransu na haɗin kai na duniya, suna taimakawa wajen rage taimakon duniya.
Rage tallafi ba kawai gazawar jagoranci na ɗabi’a ba ne kawai, bahagon tunanin ne kuma gurguwar dabara ce.
Gaza magance talauci da rashin kwanciyar hankali, da matsalolin lafiya a duniya ba abin da suke jawowa illa ƙara zurfafa rashin tsaro a duniya, da haifar da ƙaura da taɓarɓarewar tattalin arziki, da rikici.
Waɗannan matsalolin ba sa mutunta iyakoki; suna yaduwa a duniya. Idan muka juyawa mutanen da suka fi rauni a duniya, to tamkar muna shuka irin matsalolin da nan gaba mu za su shafa ne, kuma tasirin tsananin abin ya fi shafar yara.
A shekarar 2024, mutum miliyan 120 sun rasa matsugunansu saboda yaƙi da tashin hankali, da tsangwama—kimanin adadin yawan mutanen Japan—inda ‘yan gudun hijira suka shafe fiye da shekaru goma rabonsu da yankunansu.
Sau da yawa, suna gaya mana cewa babban burinsu shi ne komawa gida. Tallafi yana taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa mutane su koma gida.
A Ukraine, mun taimaka wa iyalai kamar na Natalia* da ‘yarta Sofiya* gyara gidansu da ya lalace saboda yaƙi.
A Habasha, mun tallafa wa mata kamar Rukia* su fara ƙananan kasuwanci da sake gina rayuwarsu. Taimako yana sake gina al’ummomi, yana kawo kwanciyar hankali, kuma yana farfado da tattalin arziki.
Taimako kuma yana tallafa wa mutanen da suka maƙale sakamakon ƙaura, waɗanda ba za a iya samun mafita ba. Kamar Aliya* da Zahra*, ‘yan mata biyu a sansanin Al Hol a Syria.
Sun girma a wurin. Ba a maraba da su a ƙasashensu, fuskokinsu suna nuna alamun fata, amma idanunsu suna ba da labarin laifin da ba su aikata ba.
Rashin hangen nesa
Shawarwari na rashin hangen nesa na rage tallafi suna jawo wa duniya matsala da rashin ci gaba.
Adadin yaran da ke rayuwa a yankunan da ake rikici ya kusan ninkawa sau biyu a cikin shekaru 30 da suka gabata, yayin da kashe kuɗi na soja a duniya ya ƙaru zuwa dala tiriliyan 2.4 a shekarar 2023.
A halin yanzu, zuba kuɗaɗe don magance rikici da taimakon jinƙai yana raguwa.
An yi kira kan samar da tallafin jinƙai na duniya na 2025 inda ake neman dala biliyan 44.7 don samar da taimako na ceton rayuka ga mutum miliyan 190 a ƙasashe 32 da yankuna tara masu karɓar ‘yan gudun hijira.
Idan aka samu kuɗaɗen, hakan na nufin za a kashe kusan dala 235 ga mutum ɗaya a shekara, dala 20 a wata, ko kuma kusan senti 65 a rana, wanda ya fi ƙarancin farashin gahawa a ƙasashen Yamma da dama.
Kiran na 2024 ya samu kashi 45 cikin 100 na kuɗin da ake buƙata. Kiran cewa taimako ba shi da tasiri ba rashin gaskiya ba ne kawai, wata dabara ce ta yaudarar ra’ayin jama’a.
A Gaza da Haiti, da Sudan, ayyuka na kula da yara sun yi wa ƙungiyoyinmu yawa —wasu ma ba su kai shekarun shiga makaranta ba— waɗanda ke buƙatar tallafi ta ɓangaren kula da su da kwantar musu da hankalinsu bayan ganin abubuwan tashin hankali da suka gani.
A Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai suna nufin fakon yara kai tsaye don ɗaukarsu su saka su a cikinsu. Ba za mu iya yin watsi da waɗannan lamurran gaskiyar ba.
Zuba kuɗaɗe a taimakon jinƙai ba sadaka ba ce kawai —wajibi ne na dabaru kuma wajibi ne na ɗabi’a.
Rage tallafi zai ƙara zurfafa matsaloli, yana haifar da wani zagaye na rashin kwanciyar hankali wanda zai fi tsada a magance nan gaba.
Zaɓuka masu wahala
A yayin da ake rage kuɗaɗe, hakan na tilasta wa ma’aikatan agaji yin zaɓuɓɓuka masu wahala: Shin za mu ciyar da yara a wuraren da fari ya shafa ko kuma mu ba da kulawar lafiya ga waɗanda ke wuraren yaƙi?
Shin ambaliyar ruwa za mu magnace ko sauyin yanayi? Kowace shawara tana nufin wasu yara za su sami taimakon ceton rayuka—yayin da wasu ba za su samu ba.
Wannan abu nauyi ne a kan duk ma’aikatan agaji. Yanzu fiye da kowane lokaci.
Ƙungiyar Save the Children ta yi amannar cewa rayuwar kowane yaro tana da daraja iri ɗaya, amma gaskiyar ita ce idan aka rage kuɗaɗen tallafi to rayuka suna salwanta.
Yanayin duniya yana sauyawa, tare da sabbin madafun iko da sauyin ƙawance, da ƙara rashin tabbas. Waɗannan sauye-sauye suna kawo sabbin haɗari ga aikinmu.
Tambayar ita ce ba ko za mu iya jure ci gaba da tallafi ba—amma ko za mu iya jure rashin yin hakan. Wannan lokaci ne da ke buƙatar haɗin kai da alhakin gama-gari.
Ba tare da hakan ba, muna fuskantar haɗarin rushewar ci gaban da aka samu a rage talauci da kiwon lafiya, da ilimi a tsawon shekaru.
Gwamnatoci suna taka rawa mai muhimmanci wajen ci gaba da ƙoƙarin tallafi. Ba za mu iya sabawa da makomar da ceton wasu rayuka ke nufin amincewa da rasa wasu ba. Domin a wane dalili ake ganin rayuwa ɗaya ta fi ƙarancin daraja?
Kamar yadda wanda ya kafa mu, Eglantyne Jebb, ta taɓa cewa: “Dole ne mu taɓa tunanin duniya. Duniya ba waje ne marar tausayi ba, amma tana da rashin tabbas kuma hada-hada ta mata yawa.”
Lokaci ya yi da za a sake tunanin wata duniya inda tausayi da haɗin kai tsakanin al’ummomi suka fi rinjaye kan rashin amincewa, rashin yarda, da wariya—wata duniya inda rayuwar kowane yaro take da daraja sosai.
*An sauya sunaye don kare sirri.
Togaciya: Ra’ayoyin da marubucin ya bayyana ba lallai su dace da ra’ayoyi da fahimta, da manufofin edita na TRT Afrika ba.