DUNIYA
2 minti karatu
NASA ta ɗage dawowar 'yan sama jannatin da suka maƙale a sararin samaniya zuwa duniya
NASA ta ce akwai matsala a injin jirgin sama jannatin da aka tsara zai kwaso su, amma ita rokar da jikin jirgin ba su da wata matsala.
NASA ta ɗage dawowar 'yan sama jannatin da suka maƙale a sararin samaniya zuwa duniya
NASA ta ce akwai matsala a injin jirgin sama jannatin da aka tsara zai kwaso su, amma ita rokar da jikin jirgin ba su da wata matsala. / AFP
13 Maris 2025

An ɗage aikin ƙaddamar da jirgin sama jannatin SpaceX Crew-10 mission, wanda aka yi da nufin dawo da wasu ‘yan sama jannati biyu da suka maƙale a Tashar Bincike ta Ƙasa da Ƙasa da ke Sararin Samaniya, ISS, kamar yadda hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka NASA ta faɗa.

"Akwai matsala tattare da injin jirgin da ke doron duniyar Earth," in ji wani mai sharhi a NASA, Derrol Nail, a ranar Laraba, yana mai cewa "amma rokar da jikin jirkin duk suna lafiya."

Dole sai sabuwar tawagar ta isa Tashar ISS kafin a samu damar dawo da Butch Wilmore da Suni Williams gida duniya bayan da suka shafe bayan watanni tara a sararin samaniya.

An samu damuwa game da muhimmin tsarin hydraulic kasa da awanni hudu kafin lokacin da aka tsara don harba rokar Falcon daga cibiyar Kennedy ta NASA.

Yayin da agogon kidayar lokaci ke tafiya, injiniyoyi sun duba tsarin hydraulic da ake amfani da shi wajen sakin daya daga cikin hannayen biyu da ke rike rokar da tsarin tallafawa.

Wannan tsarin yana bukatar karkata baya kafin a harba rokar.

Har 'yan sama jannati hudu da za su yi bulaguron sun shiga jirgin suna jiran umarnin ƙarshe, amma sai jirgin ya sauko ƙasa awa guda kafin lokacin harbar ya yi.

Kamfanin SpaceX ya soke harba rokar a wannan rana. Kamfanin bai sanar da sabuwar ranar sake harba shi ba nan take, amma ya nuna cewa za a iya sake gwadawa da wuri-wuri kamar daren Alhamis.

Jinkirin dawowa

Da zarar sun isa tashar sararin samaniya, tawagar Amurka, Japan da Rasha za su maye gurbin Wilmore da Williams, wadanda suka kasance a can tun watan Yuni.

Matukan biyu na gwaji sun kasance a tashar sararin samaniya na tsawon lokaci bayan da da sabon samfurin jirgin sama jannatin Starliner na kamfanin Boeing ya fuskanci manyan matsaloli a lokacin tafiya.

Tun da fari an tsara cewa tafiyar farko ta Starliner za ta kasance ta mako guda ne kawai, amma NASA ta umarci jirgin ya dawo duniya ba tare da mutane a ciki ba kuma ta tsara komawar Wilmore da Williams zuwa gida da SpaceX.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us