NIJERIYA
2 minti karatu
Shugaban EFCC ya ƙaryata rahoton da ke cewa ya tilasta wa shugaban NNPC yin murabus
Wasiƙar da lauyan shugaban EFCC, Olatimbo Ayinde, ya aika wa People Gazette ta yi gargaɗin cewa idan jaridar ba ta janye labarin kuma ta nemi afuwa ba, shugaban hukumar zai ɗauki maka ta a kotu.
Shugaban EFCC ya ƙaryata rahoton da ke cewa ya tilasta wa shugaban NNPC yin murabus
Shugaban EFCC ya ƙaryata rahoton da ke cewa ya tilasta wa shugaban NNPC yin murabus / EFCC
7 Agusta 2025

Shugaban hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon-ƙasa, Ola Olukayode, ya ƙaryata rahoton da ke cewa ya yi garkuwa da shugaban kamfanin man Nijeriya NNPC, Bashir Bayo Ojulari, tare da tilasta masa yin murabus.

Wata sanarwar da hukumar EFCC ta fitar ranar Laraba ta ce Olukayode ya bai wa jaridar Peoples Gazette da ta wallafa labarin wa’adin sa’o’i 48 ta janye labarin tare da neman afuwa a fili daga shugaban na EFCC.

A makon jiya ne jaridar ta Peoples Gazette ta wallafa wani labari inda ta ce shugaban EFCC ya yi garkuwa da shugaban kamfanin mai na Nijeriya NNPC, Bashir Bayo Ojulari, kuma ya tilasta masa ya yi murabus bisa umarnin wata mata mai suna Olatimbo Ayinde.

Kazalika jaridar ta wallafa wani labari inda ta yi iƙirarin cewa matar shugaban ƙasa, Remi Tinubu ce ta ce ba za a ƙarɓi murabus na shugaban NNPC ɗin ba.

Sanarwar ta ambato shugaban EFCC na cewa labaran da jaridar ta wallafa za su iya bayyana shi a matsayin wani wanda ya ci amanar ƙasa ta hanyar miƙa ikon hukumarsa ta EFCC ga wata Olatimbo Ayinde wadda labaran suka yi iƙirarin cewa ta sa ya tilasta wa shugaban NNPC murabus.

Wasiƙar da lauyan shugaban EFCC, Olatimbo Ayinde, ya aika wa People Gazette dai ta yi gargaɗin cewa idan jaridar ba ta janye labarin kuma ta nemi afuwa ba, shugaban hukumar zai ɗauki mataki.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us