Gwamnatin Nijeriya ta sanar da dakatar da kafa sabbin jami’o’i da manyan kwalejojin kimiyya da fasaha da na ilimi na tarayya a duk faɗin ƙasar.
Majalisar Zartarwa ta Tarayya ce ta ɗauki wannan matakin yayin zaman da ta gudanar jiya Laraba.
Ministan Ilimi na Nijeriya Dokta Olatunji Alausa ya ce an ɗauki wannan matakin ne domin daƙile buɗe cibiyoyin ilimi barkatai a ƙasar da kuma mayar da hankali wurin inganta waɗanda ake da su a ƙasa.
Dokta Olatunji ya ce an dauki matakin ne bayan tattara wasu alkaluma da suka nuna cewa samun gurbin shiga manyan makarantu a kasar bai zama matsala ba.
Ministan ya ce matsalar ita ce yawan manyan makarantu barkatai da ake da su a kasar wadanda suka jawo matsalolin rashin amfani da makarantun yadda ya kamata don samun fa’idar da ta dace, da matsalar kayan aiki da ƙarancin ma’aikata da sauransu.
Ministan ya ce jami’o’in gwamnatin tarayya da dama ba sa cikakken aikin da aka gina su don su yi, inda ya ce akwai wadanda suke da dalibai kasa da 2,000 kuma ya ce akwai wata babbar makaranta a kasar da ke da ma’aikata 1,200 da dalibai kimanin 800.
Ya ce wannan asarar kudin gwamnati ne kawai.
Dokta Husseini Abdullahi na fannin fasaha da koyar da sana’o’i na a tsangayar ilimi da ke Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa yana goyon bayan wannan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka kuma ya ce dama can wannan mataki ne da Kungiyar Malaman Jami’a ta Kasar (ASUU) ta dade tana kira ga gwamnatin kasar ta dauka.
Masanin kan harkokin ilimin ya ce sabbin manyan makarantun da ake kirkirowa sun yi yawa kuma ya ce galibi ’yan siyasa ne suke yin hakan don kai manyan makarantu yankunan da suka fito a wani kokari na samun goyon bayan mutanensu.
Dr Husseini ya ce hatta tsofaffin jami’o’i da manyan makarantu na gwamnatin tarayya da ake da su, kudin da gwamnatin take ba su ba sa isar su wanda hakan yana cikin dalilan da suka sa kungiyar ASUU ta rika zuwa yajin aiki a shekarun baya.
Malamin jami’ar ya ce wannan mataki da gwamnati ta dauka abin a yaba mata ne kuma ya ce ya kamata ne a dakatar da ƙirƙiro wasu sabbin manyan makarantun gaba daya har sai lokacin da ake da bukata a yi hakan, ba wai dakatarwar shekara bakwai ba kawai.
Sannan Dr Husseini ya ce kamata ya yi ’yan siyasar da ke son a ci gaba da kirkiro sabbin manyan makarantu barkatai su mayar da hankalinsu kan taimakawa wajen haɓaka da bunkasa manyan makarantun da ake da su, ta yadda za su rika tsayawa da kafafunsu.