Abin da ya sa Sudan ta iya lallasa Nijeriya har ta fitar da ita daga Gasar CHAN
WASANNI
3 minti karatu
Abin da ya sa Sudan ta iya lallasa Nijeriya har ta fitar da ita daga Gasar CHANMasana harkokin wasanni a Nijeriya suna ganin Sudan ta cancanci jinjina saboda duk da yakin da ƙasar ke ciki, hakan bai sa ’yan wasanta sun karaya ba, inda suka lallasa Super Eagles ta Nijeriya da ci 4 da nema a gasar CHAN.
/ Others
13 Agusta 2025

Duk da Sudan ta yi shekara biyu cikin yaƙin basasa, tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasar ta fito da martabar ƙasar, inda ta lallasa tawagar Super Eagles ta Nijeriya da ci 4 da nema a gasar CHAN 2024.

A jiya Talata ne Sudan ta yi waje da Nijeriya daga gasar ta CHAN wadda ke gudana a kasashen Kenya, Uganda, da Tanzania, wadda gasa ce ta ƙasashen Afirka amma ta ’yan wasan da ke wasa a gida cikin nahiyar. 

Wannan ne karon farko da Sudan ta samu irin wannan babbar nasara a gasar, sannan ci 4 da ta yi Nijeriya shi ne mafi muni ga Super Eagles ta samu a gasar, har ta kai an fitar da ita tun a matakin rukuni.

Fitar da Nijeriya daga gasar ta bana na zuwa ne saboda ƙasar ta buga wasanni biyu cikin uku a rukunin D, kuma duka ta sha kashi. A wansanta na farko a gasar, Senegal ta ci Nijeriya da ci 1-0.

Rashin maki

A yanzu Nijeriya ba ta da maki ko guda, kuma ba ta zura ko da ƙwallo ɗaya ba. Sudan ce ke saman teburin rukunin na D da maki 4, sai Senegal mai biye mata ita ma da maki 4, sai Congo ta uku da maki 2, sai Nijeriya wadda take ta ƙarshe da maki 0.

Duk da cewa Nijeriya tana da sauran wasa ɗaya da ya rage wanda za ta buga da Congo a ranar Talata mai zuwa, amma duk abin da ya faru a wasan ba zai canja makomar ƙasar a gasar ba.

Masana harkokin wasanni da dama suna ganin Sudan ta cancanci jinjina saboda duk da yaƙin da ƙasar ke ciki hakan bai sa ’yan wasanta sun karaya ba, musamman ta fuskar yin duk shirye-shiryen da suka kamata na halartar gasar.

Batun kocin tawagogin Nijeriya da na Sudan shi ne ake ganin babban dalilin rashin nasarar Nijeriya.

Kocin Sudan, James Kwesi Appiah wani zaƙaƙurin koci ne ɗan asalin Ghana wanda a baya ya jagoranci tawagar Ghana sau biyu, kuma shi ne kocin Black Stars ɗan Ghana na farko da ya kai su gasar kofin duniya ta FIFA a 2014.

Dalilin karaya

Shi kuwa kocin Nijeriya, Eric Chelle ɗan asalin Afirka ta Kudu ne kuma tsohon kocin Mali ne, wanda Nijeriya ta kawo bayan sallamar kocinnta na gida Augustine Eguavoen.

Bayan wasan, Chelle ya ce tawagar Nijeriya ta rasa duk wani buri, kuma wannan ne wasa mafi muni da ya taɓa jagoranta, inda ya ɗora alhakin rashin nasarar kan ‘yan wasa wajen 8 da ya ce sun bar tawagar zuwa ƙasashen waje gabanin fara gasar”.

A cewar Mataimakin Sakataren Ƙungiyar Marubuta Labarin Wasanni reshen jihar Kano, Muzzammil Dalha Yola, har yanzu a lig ɗin Nijeriya babu zaƙaƙuran ’yan wasa da za su iya gogayya da takwarorinsu na sauran ƙasashen Afirka.

Ya bayar da misali da cewa ’yan wasan tawagar Super Eagles 8 zuwa 9 an ɗauko su ne daga ƙungiya ɗaya, wato Remo Stars wanda Muzzammil ya ce zai fi kyau a ce an ɗauko ’yan wasan tawagar ne daga ƙungiyoyi daban-daban da ke buga Gasar Premier ta Nijeriya.

Sannan Muzzammil Yola ya ce ya kamata a samar da tsarin shigowa da fitar da ’yan wasa a tawagar, ta yadda sabbin jini za su riƙa maye gurbin tsofaffin ’yan wasa Super Eagles da ke buga wasan a gida.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us