NIJERIYA
2 minti karatu
Amurka ta amince a sayar wa Nijeriya makamai da bamabamai da rokoki da suka kai naira biliyan 532
Tuni hukumar DSCA mai kula da tsaron Amurka tare da manufofin ƙasashen wajen ƙasar ta miƙa takardun shaidar da ake buƙata don sanar da Majalisar Dokokin Amurka game da yiwuwar sayar da makaman.
Amurka ta amince a sayar wa Nijeriya makamai da bamabamai da rokoki da suka kai naira biliyan 532
Sanarwar ta ce makaman da kuɗinsu zai kai dala miliyan $346 sun haɗa da bamabamai da rokoki waɗanda ke kai hari bisa saiti. / Reuters
17 awanni baya

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta amince da yiwuwar sayar wa Nijeriya makamai da bamabamai da rokoki na kimanin dala miliyan 346 (kimanin naira biliyan N532), in ji ma’aikatar tsaron Amurka, Pentagon.

Tuni hukumar DSCA mai kula da tsaron Amurka tare da manufofin ƙasashen wajen ƙasar ta miƙa takardun shaidar da ake buƙata don sanar da Majalisar Dokokin Amurka game da yiwuwar sayar da makaman.

“Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta yanke hukuncin amincewa da yiwuwar sayar da makamai ga sojin ƙetare zuwa ga gwamnatin Nijeriya, in ji wata sanarwa.

Sanarwar ta ce makaman da kuɗinsu zai kai dala miliyan $346 sun haɗa da bamabamai da rokoki waɗanda ke kai hari bisa saiti.

“Hukumar kula da tsaro da manufofin ƙetare ta miƙa takardar shaidar da ake buƙata wajen sanar da Majalisar Dokokin Amurka game da yiwuwar sayar da makaman a yau (Laraba),” in ji sanarwar.

Rashin tsaro a Nijeriya ya kasance ɗaya daga cikin gagaruman ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta, inda matsalar hare-haren ɓarayin daji da ‘yan ta’adda na Boko Haram da ISWAP da ‘yan a-waren Biafra a kudu maso gabashin ƙasar ke ci gaba da matsa wa fararen hula da jami’an tsaro.

Barazanar masu tayar da ƙayar bayan ta janyo asarar rayuka da dama da raba mutane da gidajensu da katse harkokin noma da kasuwanci tare da ɗaura matsanancin nauyi kan dakarun tsaro.

Huldar tsaron Nijeriya da Turkiyya ma na taimaka wa ƙasar ta yammacin Afirka wajen yaƙar ta’addanci, inda Nijeriya take amfani da makamai da jiragen yaƙin da ta saya daga Turkiyya wajen kare fararen-hula a ƙasar.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us