AFIRKA
2 minti karatu
Adadin waɗanda suka mutum a hatsarin kwale-kwale a Jamhuriyar Kongo ya kai 148
Gobara ce ta tashi a cikin kwale-kwalen na katako mai ɗauke da kusan mutum 500 sakamakon abinci da wata mata ke dafawa a ciki, lamarin da ya jawo kwale-kwalen ya kife.
Adadin waɗanda suka mutum a hatsarin kwale-kwale a Jamhuriyar Kongo ya kai 148
Ana yawan samun hatsarin kwale-kwale a Kongo / Reuters
19 Afrilu 2025

Adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa 148 a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo a farkon makon nan, in ji wani jami'in hukumar a ranar Juma'a.

Hadarin ya afku ne da yammacin Talata a Mbandaka da ke lardin Equateur.

Sen. Jean-Paul Boketsu Bofili na lardin Equateur ya ce mutane 500 ne ke cikin jirgin ruwan na katako a lokacin da ya kife bayan ya kama wuta.

Wadanda suka mutu sun hada da kananan yara, kamar yadda ya shaida wa manema labarai, ya kara da cewa ɗaruruwan mutane ne ba a san inda suke ba, yayin da aka ceto fiye da 150 inda aka same su da ƙuna a jikinsu.

Ya ce an gano gawawwakin mutane da dama da suka ƙone daga cikin jirgin.

Tafiya zuwa kasuwa

Kafofin yada labarai sun ruwaito cewa gobarar ta tashi ne a lokacin da wata mata ke dafa abinci a cikin jirgin.

A baya dai hukumomi sun ce adadin wadanda suka mutu ya kai 50.

Jirgin na HB Kokolo ya kasance yana jigilar fasinjoji daga tashar jiragen ruwa ta Bolenge da ke lardin Equateur zuwa wata babbar kasuwa a ƙauyen Ngbondo da ke samar da kayayyaki ga yankuna da dama, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito.

Ana yawan amfani da sufurin jirgin ruwa a Kongo sakamakon rashin kyawun hanyoyi.

Hatsarin ya faru ne kwanaki bayan mutane fiye da 50 sun mutu bayan da wani kwale-kwale da ya kife da su a a cikin kogin.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us