SIYASA
2 minti karatu
'Yan sanda sun kama kusan mutum 300 kan zargin tayar da hargitsi a zaɓukan cike gurbi a Kano
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ranar Asabar ya ce mutanen da aka kama suna ɗauke da muggan makamai, ciki har da bindigogi.
'Yan sanda sun kama kusan mutum 300 kan zargin tayar da hargitsi a zaɓukan cike gurbi a Kano
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ranar Asabar ya ce mutanen da aka kama suna ɗauke da muggan makamai / AP
14 awanni baya

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta ce ta kama mutum 288 bisa zargin tayar da hargitsi a yayin da ake gudanar da zaɓukan cike gurbi a wasu mazaɓu na Jihar.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Ya ce mutanen kama suna ɗauke da muggan makamai, ciki har da bindigogi da aka yi a gida da wuƙaƙe da adda da sauransu.

‘Fafatawa mai zafi’

A ranar Asabar ɗin nan ne ake gudanar da zaɓukan cike gurbi a mazaɓu goma sha shida a jihohi 13 - Adamawa, Anambra, Edo, Enugu, Jigawa, Kaduna, Kano, Kogi, Neja, Ogun, Oyo, Taraba da Zamfara.

Sai dai fafatawar tana yin zafi a jihohi irin su Kano da Kaduna sakamakon mummunar adawar da ke tsakanin wasu manyan ‘yan siyasar jihohin.

A Jihar Kano inda Jam’iyyar NNPP take mulki, an ja zare tsakaninta da Jam’iyyar APC wadda aka kayar a zaɓen shekarar 2023.

Kazalika a Jihar Kaduna, tsohon gwamnan Jihar Nasir El-Rufai wanda ke goyon bayan ‘yan takarar Jam’iyyun ADC da SDP, yana ƙoƙarin kayar da ɗan takarar Jam’iyyar APC wadda tsohon abokinsa kuma mutumin da ya gaje shi, Gwamna Uba Sani yake ƙoƙarin ganin ta kai gaci.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us