SIYASA
2 minti karatu
Ana gudanar da zaɓukan cike gurbi a wasu jihohin Nijeriya
Manyan 'yan siyasa irin su gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da takwaransa na Kaduna Uba Sani da babban abokin hamayyarsa kuma tsohon gwamnan Jihar ta Kaduna Nasir El-Rufai duka sun yi yaƙin neman zaɓe ga 'yan takarar jam'iyyunsu.
Ana gudanar da zaɓukan cike gurbi a wasu jihohin Nijeriya
Masana na kallon zaɓukan a matsayin zakaran gwajin dafi na babban zaɓe mai zuwa / Reuters
18 awanni baya

A ranar Asabar ɗin nan ne ake gudanar da zaɓukan cike gurbi a wasu mazaɓu da ke sassa daban-daban a faɗin Nijeriya, waɗanda ake gani za su ƙara fito da ƙarfi ko akasin haka na Jam’iyyar APC mai mulki da kuma Jam’iyyun adawa na ƙasar.

Ana gudanar da zaɓukan ne a mazaɓu goma sha shida a jihohi 13 - Adamawa, Anambra, Edo, Enugu, Jigawa, Kaduna, Kano, Kogi, Neja, Ogun, Oyo, Taraba da Zamfara.

Zaɓukan da za a cike gurbinsu sun haɗa da na ‘yan majalisar dattawa da majalisar wakilai da majalisun dokoki na jihohi.

Ana yin zaɓukan ne sakamakon mutuwar waɗanda ke kan kujerun ko kuma sauka daga kujerun saboda wasu dalilai.

Manyan 'yan siyasa irin su gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP da ɓangaren APC da ke ƙarƙashin tsohon gwamnan Jihar Abdullahi Ganduje; da gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani na Jam’iyyar APC da babban abokin hamayyarsa kuma tsohon gwamnan Jihar ta Kaduna Nasir El-Rufai da ya yi kamfe ga ‘yan takarar Jam’iyyun ADC da SDP duka sun yi yaƙin neman zaɓe ga 'yan takarar jam'iyyunsu.

Masana harkokin siyasa na ganin za a yi fafatawa mai zafi tsakanin waɗanda manyan ‘yan siyasa waɗanda dukansu suke son nuna cewa su ne suke da ƙarfin faɗa-a-ji a waɗannan jihohi.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us