Kisa don zaman lafiya: Yadda shugabanni ke kare ta’annati da sunan kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe
DUNIYA
7 minti karatu
Kisa don zaman lafiya: Yadda shugabanni ke kare ta’annati da sunan kawo ƙarshen yaƙe-yaƙeDaga kutsawa Iraki zuwa ga jefa bam a Hiroshima da kisan kare dangi a Gaza, tuni shugabanni suke yada cewa shan wahalar mutane da dama “muguntar dole ce” don samar da zaman lafiya.
Makusantan Falasdinawan da Isra'ila ta kashe na jimamin mutuwar 'yan uwansu. / AA
18 awanni baya

Lokacin da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi iƙirari a makon da ya gabata cewa mamaye Gaza ita ce hanya ɗaya tilo ta "kawo ƙarshen yaƙi," ya sanya shi shiga jerin jagororin da ke son a yi yaki kuma suke bayyana rasa rayukan fararen hula da dama a matsayin abin da zai kawo zaman lafiya.

Tun daga harin bama-bamai da Amurka ta kai a Hiroshima da Cambodia zuwa mamaye Iraki, kalaman dai duk iri guda ne.

"Wannan mummunar ɗabi'a ce," in ji Na'eem Jeenah, babbar mai bincike a Cibiyar Mapungubwe kuma Babbar Darakta a Cibiyar Nazarin Afirka-Gabas ta Tsakiya, "inda shugabanni ke ƙoƙarin nuna kansu a matsayin masu neman zaman lafiya, wadanda suke yaka kuma a matsayin wadanda ba sa son zaman lafiyar, ko ma kiran su ‘yan ta’adda masu son zubar da jini.”

"Sau da yawa, mafi yawan jama'a, musamman a ƙasashensu, suna yarda da su. Ƙungiyoyin haɗin gwiwa suna nuna amanna da matakan, kuma sai lokacin da jama'a a gida da waje suka ƙi amince wa da yaudarar ne labarin ya fara rugujewa," Jeenah ta shaida wa TRT World.

Jeenah ta bayar da hujjar cewa wannan shi ne ainihin abin da ke faru wa a kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Gaza.

"Mutane kalilan ne a duniya, in ban da wadanda ke goyon bayan Isra'ila ba tare da kakkautawa ba, suka yi imanin cewa tana yaki da 'ta'addanci' ko kuma laifinta ya fara ne a ranar 7 ga Oktoban 2023.

Hatta kawayen Isra'ila, ko sun yarda ko ba su yarda ba, ba su amince da labarin da take bayarwa ba."

‘Muguntar dole’ a tsawon tarihi

Idan aka zo ga fadin “muguntar dole”, Amurka ce ta sami kanta cikin yanayin yin kiraye-kiraye marasa kyau don “ceton rayuka.”

A watan Agustan 1945, Shugaba Harry Truman ya bayar da izinin jefa bama-bamai a Hiroshima da Nagasaki, yana mai da'awar cewa hare-haren za su gaggauta kawo karshen yakin duniya na biyu da kuma ceton dubban daruruwan rayuka.

Bama-Baman sun kashe kusan mutane kwata miliyan, kuma sun bar wadanda suka tsira da raunukan jiki da na kwakwalwan tsawon shekaru.

Masana tarihi da yawa tun daga lokacin sun yi nuni da cewa Japan ta riga ta kasance a kan gaɓar mika wuya, musamman bayan da sojojin Soviet suka shiga yaƙi, wanda hakan ya sa tashin bama-bamai gaza zama abinda zai kawo ƙarshen yaƙi cikin sauri, kuma ya zama mai kokarin karfafa karfin fada a jin Amurka a yankin bayan yaƙin.

Jeenah ta lura da cewa wannan zaɓin na bayyana matsayin launin fata wajen yanke shawara a lokacin yaƙi. 

"Manyan abokan gabar Kawancen kasashe su ne Nazi da ke Jamus, amma duk da haka ba a jefa bama-bamai a Turai ba; an jefa su a Japan, inda wariyar launin fata ya biyo baya. Za a iya gwada jikkunan ‘yan kasar Japan da sababbin makamai saboda ba su da daraja daidai da fararen fata."

Kasa da shekaru ashirin bayan haka, Shugaba Richard Nixon da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro Henry Kissinger sun ba da umarnin yin gangamin tayar da bama-bamai a asirce a Cambodia, wai da sunan hanyar “gajarta yaki” a Vietnam.

Maimakon haka, hare-haren sun hargitsa Cambodia, sun kashe dubun-dubatar fararen hula, kuma sun bayar da gudunmawa ga yanayin da ya bayar da damar kisan kare dangi na Khmer Rouge.

Matakin da ake kira da na gaggawar kawo zaman lafiya shi ne kai tsaye ya share fagen kawo daya daga cikin munanan laifuka da aka aikata a karni na 20.

Hakazalika, a 2003, Amurka ta mamayi Iraki a ƙarƙashin da’awar kawar da makaman kare dangi da 'yantar da 'yan kasar Iraki daga mulkin kama-karya na Saddam Hussein.

Ba a taɓa samun irin waɗannan makaman ba a kasar. Maimakon haka, yaƙin ya hambarar da mulkin don kawai a kawo hargitsi na tsawon shekaru, tashin hankalin addini, da gudun hijira.

Duniya ta shaida irin munanan abubuwan da suka faru a gidan yarin Abu Ghraib, inda wasu hotuna da aka fitar suka nuna cewa sojojin Amurka na azabtar da fursunonin da ake tsare da su, da kuma wulakanta wadanda ake tsare da su, wata babbar mummunar alama ce ta yaki da aka bayyana a matsayin wajibi.

Kalaman Netanyahu game da Gaza sun yi daidai da wannan al'ada: bayyana matakan soji masu tsauri a matsayin abinda ya zama dole duk da ba a so, ana bayyana hakan a matsayin shinge na karshe kafin a samu zaman lafiya, da bayyana farar hular da aka rutsa a matsayin kayan tsautsayi ko makiya da ake hada baki da su.

A cewar Jeenah, wannan wani bangare ne na “yaki mai cike da labari”.

"A Falasdinu, gwamnatin Isra'ila ta kwashe shekaru da yawa tana amfani da wanzuwar 'yan gwagwarmayar Falasdinu - ko na PLO, Fatah, PFLP, Hamas ko kuma wasu daban - wadanda za su yi kisa, fyade da kuma satar kayan jama’a."

"Ko da wannan labarin bai zama gaskiya ba, suna haifar da jerin gwanon karya don ganin ya zama hakan, kamar yadda muka gani a sakamakon harin 7 ga Oktoba da tirjiya a Gaza," in ji Jeenah.

Babu madogara a karkashin dokokin kasa da kasa

Dokokin kasa da kasa sun haramta kai hare-hare kan fararen hula da gangan kuma sun bukaci a kare ma'aikatan jin kai da wadanda ba mayaka ba.

Batun aikata ta'annat "don kawo karshen yaki" ba shi da wata madogara a karkashin shari’a..

"Wannan batu haka yake musamman ma a ƙarƙashin Yarjejeniyar Geneva (1949) da ƙarin ƙa'idodinsu. Irin waɗannan ayyukan na ci gaba da zama wandanda za a gurfanar da masu aikata su a gaban shari’a - a gaban kotun ICC, kotunan wucin gadi, ko kotunan ƙasa da ke ƙarƙashin ikon kasashe," in ji Jeenah.

"Duk wata da'awar cewa matakin soji na da manufar takaita yaki, dole ne a auna shi da ka'idojin bambance-bambance da daidaito.

“Ba za a iya tabbatar da kai hari ga farar hula da gangan, azabtarwa, ko wasu laifukan yaki ba ta hanyar da'awar 'hakan wajibi ne'."

Ka'idodin bambance-bambance da daidaito a cikin dokokin rikicin makamai na buƙatar rage cutar da fararen hula, kuma ba za a taɓa amfani da su a matsayin hanyar kawo ƙarshen rikici ba.

Amma duk da haka, kamar yadda Jeenah ta nuna, Isra’ila ta yi aika-aika ba tare da fuskantar wani hukunci ba, da sanin cewa kasashen yammacin duniya za su kare ta ko dada gurfana a gaban kotunan kasa da kasa ne.

Kirkirar amincewa da rikii

Domin ganin ta'asar ta zama abin jin daɗi, shugabanni suna zuba hannun jari sosai wajen tsara labari. Kalmomi irin su "mutuwar dole," "sadaukarwar tilas," ko "harin tiyata" na nuna halascin rikici.

Lokacin da batutuwan suka dakata, har ma bayan shekaru da yawa, yawancin Amurkawa suna kare harin bama-baman din da aka kai Hiroshima da Nagasaki a matsayin wajibi. A 1945, kashi 85 cikin ɗari ne suka nuna amincewa da harin.

Ya zuwa 2015, amincewar ta ragu zuwa kashi 46, kuma a shekarar 2024, sama da kashi uku na Amurkawa sun ce bai kamata a ce hakan ya faru ba gaba daya.

Wata babbar dabara ita ce dasa tsoro a zukatan jama’a, a cewar Jeenah.

"Bayan harin 9/11, Amurka ta kirkiri tsoro wanda ya sa Amurkawa suka yarda da ba kawai tauye hakkin wasu a kasashen waje ba har ma da 'yancin kansu a cikin gida; balle ma hakkokin mutanen Afghanistan, Pakistan, ko Larabawa, waɗanda ƙasashensu suka zama filin wasan ayyukan sojin Amurka."

Sau da yawa ana kara karfafa wannan tsoro ta hanyar bayyana fifiko.

Jeenah ta kara da cewa "Ko dai Amurkawa suna tunanin cewa su wasu mutane ne na daban, ko fararen fata sna ganin sun fi sauran mutane daraja, ko kuma Yahudawan Isra'ila suna ganin cewa su mutane ne da Allah ya zaba, tunanin duk iri daya ne: jin dadin rukunin da aka fifita, ya fi rayuwar wadanda aka kaskantar muhimmanci" in ji Jeenah.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us