Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa ambaliyar ruwa ta kashe mutum 23 tare da jikkata 21 yayin da ta raba mutum 42,000 da gidajensu.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito cewa hukumar kwana-kwana ta ƙasar (GNSP) ce ta bayyana hakan a wani taron maneman labarai da ta gabatar ranar Alhamis.
A sanarwar da ta fitar a taron, GNSP ta ce ambaliya ta rusa gidaje 361. Sai dai ba ta faɗi lokacin da lamarin ya faru ba.
Kazalika GNSP ta tuna wa mutane shawarwarin da ta bayar a baya game da matakan da ya kamata a ɗauka wajen kauce wa hatsarin ambaliyar musamman ƙaurace wa tsallake gadajojin da ruwa ya rufe da kuma barin wuraren ambaliya da kuma rashin zama a gidaje masu rauni.
Ta kuma gargaɗi mutane game da fakewa ƙarƙshin bishiyoyi da toshe magudanan ruwa da linƙaya a a cikin ƙududdufi da kuma tono bayan ayi ruwa
"An buƙaci direbobi su yi tafiya madaidaici a lokacin da ake ruwa kuma su ƙaurace wa shiga hatsarin da zai zama dole ba.
“Idan aka ga abu mai hatsari, ya kamata mutane su nemi mafaka tare da kiran lamba 16 domin sanar da masu tataimakon gaggawa da kuma hukumomi," in ji sanarwar.
Daga bisani hukumar ta shawarci masu gine-gine su bi dokoki gine-gine wajen zaɓen kayan gini da kuma bin sharuɗɗa.