Ƙungiyar ƙwadago ta direbobin tirelolin dakon mai a Nijeriya (NUPENG) ta yi shelar dakatar da shirinta na soma yajin aikin bayan ta ƙulla yarjejeniya da shugabannin matatar mai ta Dangote kan amincewa da ‘yancin ma’aikata na shiga ƙungiyoyin ƙwadago.
An cim ma yarjejeniyar ce a wata tattaunawar sirri da hukumar tsaro ta farin kaya ta ƙasar (DSS) ta jagoranta kuma Ministan Kuɗi da wakilan ƙungiyar ƙwadagon Nijeriya suka halarta.
Muƙaddashin sakataren NLC, Benson Upah, ne ya tabbatar da sakamakon tattaunawar yayin da ma’aikatar ƙwadagon Nijeriya ta ce za ta fitar da sanarwa a hukumance nan ba da jimawa ba.
An cim ma wannan matsaya ne a tattunawar da ma’aikatar ƙwadagon tarayya ta jagoranta ranar Litinin 8 ga watan Satumba bayan NUPENG tayi barazanar soma yajin aiki kan yadda kamfanin ya ƙi amincewa da ‘yancin ma’aikatansa na shiga ƙungiyar ƙwadago.
Fahimtar Juna
Bisa ga yarjejeniyar fahimtar juna da aka rattaba wa hannu a zaman, ɓangarorin biyu sun amince cewa shiga ƙungiyar ƙwadago ‘yanci ne da ke cikin dokokin ƙwadago, kuma za a bai wa ma’aikatan matatar man Dangote da ke son shiga ƙungiyar damar yin hakan.
Yarjejeniyar ta kuma bayyana cewa tsarin shiga ƙungiyar ƙwadagon zai fara nan-take ne kuma za a kammala shi cikin mako biyu.
Kazalika yarjejeniyar ta ce babu wanda za musgunawa cikin ma’aikatan matatar man Dangote sakamakon barazanar shiga yajin aikin.
Bisa yarjejeniyar, ƙungiyar NUPENG ta dakatar da yajin aikinta nan-take yayin da ake sa ran ɓangarorin biyu su sanar da Ministan Ƙwadago halin da ake ciki mako ɗaya bayan an kammala batun.