'Yan Nijeriya na tattaunawa kan batun harajin man fetur da dizal na kashi 5 cikin 100
NIJERIYA
3 minti karatu
'Yan Nijeriya na tattaunawa kan batun harajin man fetur da dizal na kashi 5 cikin 100Gwamnati ta ce da ma can akwai dokar cikin dokokin hukumar da ke kula da gyaran tituna ta ƙasa wato FERMA tun daga shekarar 2007, kawai a yanzu an mayar da ita ne cikin sabbin dokokin haraji na Nijeriya na 2025.
Cikin manyan matakan da Tinubu ya fara dauka bayan hawansa mulki har da cire tallafin man fetur da karya darajar naira / Nigeria Presidency
11 awanni baya

‘Yan Nijeriya suna ci gaba da tattaunawa da neman ƙarin haske a kan matakin gwamnatin ƙasar na fara karɓar harajin kashi biyar cikin 100 kan man fetur da dizal.

Idan za a tuna a watan Yunin bana ne gwamnatin Nijeriya ta rattaba hannu kan sabbin dokokin haraji da suka jawo ce-ce-ku-ce musamman tsakanin yankin arewaci da kuma kudancin kasar, kuma za su fara aiki ne a watan Janairun shekara mai zuwa ta 2026.

Sai dai ’yan kasar da dama suna nuna damuwa kan harajin kaso 5 cikin 100 na man fetur da dizal da gwamnati take shirin fara karba, wanda damuwar ba ta rasa nasaba da matsin tattalin arziki da tsadar da rayuwa da ake ta fama da su a kasar a halin yanzu.

Ko da yake gwamnati ta buƙaci ’yan kasar da su kwantar da hankalinsu tare da cewa wannan ba sabon haraji ba ne.

Gwamnatin ta ce da ma can akwai dokar cikin dokokin hukumar da ke kula da gyaran tituna ta ƙasa wato FERMA tun daga shekarar 2007, kawai a yanzu an mayar da ita ne cikin sabbin dokokin haraji na Nijeriya na 2025.

Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa da ke tsare-tsare da yi wa tsarin haraji garambawul, Mista Taiwo Oyedele ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X cewa harajin man fetur din ba sabon haraji ba ne da ake zargin gwamnatin Tinubu ta ƙirƙiro.

Ya ce wannan tanadi tuni yana cikin dokar hukumar da ke kula da gyaran tituna ta ƙasa wato FERMA Act 2007, kawai an sake haɗe ta ne cikin sababbin dokokin haraji na Nijeriya na 2025.

Mutane na cewa gwamnati za ta fara karɓar harajin man fetur din daga watan Janairun shekarar 2026. Amma Mista Taiwo ya ce ba a tsayar da ranar da shi wannan harajin fetur din zai fara aiki ba tukuna.

Ya ce duk da an sanya shi cikin sabbin dokokin haraji, hakan ba ya nufin za su fara aiki tare ba.

Mista Taiwo bai bayyana taƙamaiman lokacin da za a fara karbar wannan harajin ba, amma ya ce bisa ga sabuwar doka, Ministan Kudin Ƙasar ne kadai zai iya bayar da izinin fara aiwatar da harajin, kuma sai an wallafa a mujallar gwamnatin tarayya mai ɗauke da dokoki wato ‘Official Gazette’, kafin ya fara aiki.

A hannu guda kuma kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito Ministan Kudin Wale Edun yana cewa gwamnati tana sane da halin matsin tattalin arziki da ’yan ƙasar suke ciki kuma ba za a fara karbar harajin ba tukuna.

Kazalika gwamnatin kasar ta yi karin haske kan kayayyakin makamashin da harajin zai shafa, inda ta ce man fetur da man gas na dizal ne za a ɗora wannan ƙarin haraji a kansu.

Amma sauran muhimman kayayyakin makamashi da ake amfani da su a gidaje kamar su kalanzir da gas din girki da kuma iskar gas ta CNG ba su shiga cikin wannan ƙarin harajin ba.

Na na san wani zai ce makuɗan kuɗaɗen harajin da gwamnati za ta samu me za a yi da su?

Gwamnatin ta bayyana cewa duk kuɗaɗen da aka tara daga wannan ƙarin haraji zai tafi ne cikin asusu na musamman da aka ware don gina hanyoyi da gyara su, kamar yadda Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa da ke tsare-tsare da yi wa tsarin haraji garambawul, Mista Taiwo Oyedele ya bayyana.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us