Hukumar da ke kula da hanyoyin ruwa ta ƙasa a Nijeriya (NIWA) ta sanya dokar hana zirga-zirgar kwale-kwale waɗanda ba su da lasisi da kuma lodi a wuraren da ba su da izinin yin hakan, a wani mataki na daƙile yawan haɗurran jiragen ruwa tare da kare rayukan al’umma a faɗin ƙasar.
Babban daraktan hukumar ta NIWA, Bola Oyebamiji, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata.
A cewarsa, daga yanzu ba za sake barin wani kwale-kwalen fasinja da ake biyan kuɗi ya yi lodi a tasha ko wurin da NIWA ba ta amince da shi ba.
Hanyoyin ruwa masu hatsari: Dalilan da ke sa Nijeriya fuskantar hatsatsin jiragen ruwa a-kai-a-kai
Kazalika ya jaddada cewa dole ne a bayyana sunayen dukkan kwale-kwale da kuma wuraren da suka yi lodi, yayin da su kuma masu gudanar da zirga-zirgarsu dole su samar da kuma tilasta yin amfani da rigunan kariya a ko yaushe.
“NIWA ta sanya dokar hana yin lodi daga dukkan wuraren da ake yin lodin da ba sansu ba ko kuma ba su da izinin yin haka a faɗin ƙasar nan, ba za a bari wani kwale-kwale ya ɗauki fasinja ko ya yi lodi daga kowane wuri da NIWA ba ta amince ko kuma ta yi wa rajista ba,’’ a cewar Oyebamiji.
Matakin hakan dai ya biyo bayan wasu munanan hatsarin kwale-kwale da suka afku a watannin baya-bayan nan Nijeriya.
Asarar rayuka
A watan Afrilun bana, wani kwale-kwale ɗauke da wasu ‘yan kasuwa ya kife a Kogin Neja a garin Lapai na Jihar Neja lamarin da ya yi sanadin mutuwar fasinjojin ciki gaba ɗaya.
Kazalika a watan Yuli, an yi asarar rayuka 15 a wani hatsarin kwale-kwale a Shiroro da ke Jihar ta Neja, yayin da aka fuskanci munanan haɗurran kwale-kwale a Jihar Sokoto a tsakanin watan Agusta zuwa Satumban nan waɗanda duk suka yi sanadin mutuwar mutane da dama ko kuma ba a gansu ba.
A baya bayan nan shi ne, nutsewar wani kwale-kwale ɗauke da mutum 27 waɗanda ke hanyarsu ta zuwa gaisuwar ta’aziyya daga tashar ruwan Kainji da ke Borgu a Jihar Neja.
Ƙwararru dai danganta irin wannan bala'o'in da suke faruwa da rashin bin ƙa'idoji da kuma rashin bin matakan tsaro, lamarin da hukumar NIWA ta ce an tsara wasu sabbin ƙa'idojin da matakai da za su magance matsalar.