SIYASA
2 minti karatu
INEC ta buƙaci a hukunta duk wanda ya fara kamfen ɗin 2027 kafin lokaci
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta Nijeriya (INEC) ta bukaci da a yi sauye-sauyen dokoki da daukar matakai masu tsauri kan ‘yan siyasa da jam’iyyun siyasa da suke fara gangami da wuri tun kafin lokacin manyan zabukan 2027 ya zo.
INEC ta buƙaci a hukunta duk wanda ya fara kamfen ɗin 2027 kafin lokaci
Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) / TRT Afrika Hausa
7 awanni baya

Shugaban Hukumar ta INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, a yayin da yake magana a Abuja, a wajen wani taro kan kalubalen yakin neman zabe da wuri, ya koka kan yadda hukumar ba ta da hurumin hukunta masu laifi.

Yakubu ya bayyana damuwarsa da cewa ‘yan siyasa da ‘yan takararsu sun jefa al’ummar kasar cikin “dawwamammiyar kakar zabe,” wanda hakan ya saɓa wa sashe na 94(1) na dokar zabe ta 2022, wanda ya ba da damar yakin neman zabe kwanaki 150 kacal kafin zaben.

Duk da wannan doka, shugaban na INEC ya yi tsokaci da cewa ’yan siyasa na ci gaba da mamaye wuraren jama’a da tallace-tallacen kafafen yada labarai, da gangami, da allunan ttallace-tallacen takarar zabukan 2027 da kuma zabukan fitar da gwani da ke tafe.

Ya ce an kira taron ne domin a bukaci ‘yan majalisar dokoki, kungiyoyin farar hula, masu kula da harkokin shari’a da kuma masana harkokin shari’a su lalubo bakin zaren.

Shugaban na INEC ya bayyana kwarin gwiwar cewa majalisar dokokin kasar da a halin yanzu take nazari kan dokar zabe, za ta yi aiki da shawarwarin da za su ƙarfafa aiki da dokar.

Da yake goyon bayan matsayinsa, Shugaban Cibiyar Gudanarwa da Zabe ta INEC, Farfesa Abdullahi Abdu Zuru ya yi gargadin cewa idan ba a magance hakan ba, to za ta iya kawar da hankalin shugabanni daga harkokin mulki da kuma zubar da mutuncin jama’a.

Shi ma da yake nasa jawabin, tsohon shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Attahiru Jega ya yi gargadin cewa yawaitar yakin neman zabe, wanda galibin masu rike da madafun iko da wasu ‘yan jam’iyya ne ke bayar da kudade ta hanyoyi marasa kyau, na iya kawo cikas ga sahihancin zaben 2027.

Taron wanda ya samu halartar shuwagabannin jam’iyyun siyasa, kungiyar lauyoyin Nijeriya, hukumar kula da harkokin yada labarai ta kasa (NBC), da hukumar kula da harkokin tallace-tallace ta Nijeriya (ARCON), da kungiyoyin farar hula, da masu ruwa da tsaki a harkokin yada labarai, ya cim ma matsayar cewa tsaftace harkokin zabukan Nijeriya na bukatar gyara cikin gaggawa, da daukan tsauraran matakan tsaro, da kuma karfafa ilimantar da al’umma.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us