Uwargidan Shugaban Ƙasar Turkiyya Emine Erdogan ta bayyana a dandalin NSosyal ko NEXT Sosyal, sabon dandalin sada zumunta na ƙasar Turkiyya da aka kaddamar, tare da mika sakon jin daɗi da godiya.
"Barkanmu da war haka daga NSosyal. Na yi farin cikin kasancewa cikin wannan dandali namu na gida, na ƙasarmu, da masu zaman kansu, kuma ina mika godiyata ga duk wanda ya kawo wannan alfahari ga al'ummarmu,” ta faɗa a saƙonta na farko da ta wallafa a raar Talata.
A cikin wannan amintacciyar duniyar dijital tamu, za mu yi tunani da samarwa tare, da kuma tsara makomar gaba tare da dabi'unmu. Muna shirye don sabuwar tafiya tare da NSosyal."
Hawanta dandalin na zuwa ne kwana guda bayan da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bude nasa shafin a dandalin NSosyal.
NSosyal, wanda aka haɓaka a ƙarƙashin jagorancin Turkiyya Technology Team (T3) Foundation, masu amfani da shi sun zarta miliyan ɗaya a ranar 16 ga Agusta kuma yana ci gaba da haɓaka cikin sauri.
Tun lokacin da aka ƙaddamar da dandalin, ya faɗaɗa cikin sauri, yana ba da sarari ga masu amfani don wallafa saƙonninsu da abun da ke ransu da labarai da fasaha da salon rayuwa da abubuwan da ke faruwa a yanzu.
Amincewar da Shugaban Ƙasar Turkiyya da Uwargidan Shugaban Ƙasar suka yi da shafin ya nuna wani ƙwarin gwiwa ga NSosyal, inda ya kara karfafa yunƙurin da Turkiyya ke yi na haɓaka hanyoyin sadarwa na zamani na cikin gida.