Turkiyya na hanzarta gudanar da ayyukan diflomasiyya don kawo karshen rikicin cikin gida a Libya tare da samar da “Libya mai hadin kai kuma dunkulalliya” kamar yadda majiyoyin Ma’aikatar Tsaro ta Turkiyya suka bayyana.
Kokarin ya faro ne tare da ziyarar da Kwamandan Sojojin Kasa na Libya Lutanal Janar Saddam Haftar ya kai Turkiyya a watan Afrilun 2025.
A farkon makon nan, jirgin ruwan sojin Turkiyya na TCG Kinaliada ya ziyarci tashar jiragen ruwan Tarabulus inda ya jagoranci tattaunawa tsakanin Jakadan Turkiyya a Libya, Guven Begec, da Ministan Tsaro na Libya, Shugaban Rundunar Soji, Kwamandan Sojojin Ruwa, Kwamandan Dakaurn Tsaron Iyakokin Teku da Kwamandan da ke Tarabulus.
Ana sa ran TCG Kinaliada zai ziyarci tashar jiragen ruwa ta Benghazi ranar Larabar nan, inda za a yi karamin bikin tarbar baki na soji da ziyara a hukumance.
Mataki mai dauke da dabarun zaman lafiya
Wannan ziyarar na nuni da tsarin da Turkiyya ke da shi na hada kai da samar da kwanciyar hankali ga daukacin kasar Libya, da kuma wata sabuwar alama d ake bayyana manufofinta na rungumar daukacin kasar.
A farkon makon nan TCG Kınalıada ya kai wata ziyarar aiki tashar jiragen ruwa ta Tarabuklus da ke Libya.
Bayan da ya bar tashar jiragen ruwa ta Tarabulus, ya gudanar da atisayen horaswa a teku tare da wani jirgin ruwa mai suna Shafak mallakin sojojin ruwan Libya.
A watan Afrilun 2025, Lutanal Janar Saddam Khalifa Hafter, kwamandan sojojin kasa na Libya, ya ziyarci Turkiyya, kuma ministan tsaron kasar Yaşar Güler da kwamandan sojojin kasa na lokacin, wanda a yanzu babban hafsan hafsoshin sojan kasar Janar Selçuk Bayraktaroğlu ne suka tarbe shi a Ankara.
Majiyar Ma'aikatar Tsaron Ƙasar Turkiyya ta bayyana cewa, "Turkiyya da Libya kasashe biyu ne abokan juna da ke da alaka mai zurfi ta tarihi da al'adu, tun daga farko burinmu shi ne al'ummar Libya su zauna cikin hadin kai, dunkule wa waje guda, zaman lafiya da kwanciyar hankali."