Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya wallafa saƙonsa na farko a shafinsa na NEXT Sosyal, wani sabon dandalin sada zumunta na ƙasar da ke bunƙasa cikin sauri.
Shugaban ya wallafa wani baiti daga cikin waƙar Erdem Bayazit ‘‘Soon the Day Will Rise - "A flower sprouted between concrete walls’’ wato “Ba da daɗewa ba Rana Za Ta Fito- "Fure zai yi yaɗu a tsakanin bangon kankare" - a ranar Litinin Erdogan ya tambayi mabiya daga dandalin, "Shin kun shirya?"
Bayan saƙon nasa, ya yi mafani da maudi’i “We’re starting” (mun fara) da kuma alamar tutar ƙasar Turkiyya da Duniya da kuma kumbo.
Me nene Next Sosyal?
Sakon da shugaban ya wallafa na zuwa ne a yayin da dandalin Next Sosyal, wanda aka ƙirƙire shi ƙarkashin jagorancin ‘Turkiye Technology Team (T3) Foundation’ wato tawagar gidauniyar fasaha ta Turkiyya (T3) ya samu mutane fiye da miliyan ɗaya da suke amfani shi.
A ranar Asabar ne dai Selcuk Bayraktar, shugaban hukumar gudanarwa ta TEKNOFEST kana ɗaya daga cikin kwamitin amintattu na gidauniyar T3 ne ya sanar da wannan gagarumin matakin da aka kai.
An tallata dandalin a matsayin “tsaftacce kuma amintacce” wanda zai maye sauran dandalin sada zumunta da ake da su a duniya, NEXT Sosyal ya yi saurin samun matsayi a sama inda ya zarce saura tkwarorinsa a kasuwar manhajoji na wayar hannu, a ɗan ƙanƙanin lokaci ya samu matsayin manhajar da ya yi fice wanda kuma ake sauke shi kyauta a cikin jerin sauran ‘‘manhajojin sada zumunta.’’
Tun lokacin da aka ƙaddamar shi, dandanlin yake ta bunƙasa cikin sauri, inda yake bai wa masu mafani damar bayyana ra’ayoyinsu da bayanan labarai, fasaha da salon rayuwa da kuma abubuwan da ke faruwa kai tsaye.
Amincewa da kuma nuna goyon bayan shugaban ya kara bayyana wata gaggaruma ci gaba ga NEXT Sosyal, tare da ƙarfafa yunkurin Turkiyya na haɓaka manhajoji zamani da ake samar wa na cikin gida.