DUNIYA
3 minti karatu
Fidan da Rubio sun yi nazarin sakamakon tattaunawar Washington kan kawo ƙarshen yaƙin Ukraine
Ministan Harkokin Wajen Turkiya Hakan Fidan da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio sun tattauna kan matakan da za a iya bi don kammala yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine.
Fidan da Rubio sun yi nazarin sakamakon tattaunawar Washington kan kawo ƙarshen yaƙin Ukraine
Jami'an biyu sun amince akan bukatar a dakatar da kashe-kashen da ke faruwa tsakanin kasashen biyu masu rikici. / AA
19 Agusta 2025

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, sun tattauna kan sakamakon taron da aka gudanar a birnin Washington tsakanin Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy da sauran Shugabannin Turai.

A wata tattaunawar wayar tarho da suka yi a ranar Talata, sun kuma tattauna kan sakamakon taron da aka yi tsakanin Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Rasha Vladimir Putin a Alaska a ranar 15 ga watan Agusta, kamar yadda majiyoyin diflomasiyyar Turkiyya suka bayyana.

Sun yi magana kan matakan da za a iya dauka nan gaba don kawo karshen yakin da ke tsakanin Rasha da Ukraine, inda Fidan ya bayyana cewa a shirye Turkiyya take ta bayar da duk wani irin tallafi don cim ma zaman lafiya mai adalci da ɗorewa.

A cewar mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, Tommy Pigott jami’an biyu sun amince kan bukatar dakatar da kashe-kashe tsakanin kasashen biyu da ke fada.

Ci gaba da goyon bayan zaman lafiya a Ukraine

Mataimakin Shugaban Turkiyya, Cevdet Yilmaz ya bayyana a ranar Talata cewa Turkiyya za ta ci gaba da goyon bayan shirye-shiryen diflomasiyya da nufin cim ma "zaman lafiya mai adalci da ɗorewa" a Ukraine.

"Za mu ci gaba da bayar da cikakken goyon baya ga kokarin diflomasiyya don zaman lafiya mai adalci da dorewa," in ji Yilmaz a dandalin sada zumunta na Turkiyya, NSosyal.

Yilmaz ya bayyana cewa ya halarci taron intanet na "gamayyar masu son tabbatarwa" a madadin Shugaba Recep Tayyip Erdogan a ranar Talata, bayan zaman da aka yi a ranar 13 da 17 ga watan Agusta.

"A taron na intanet, mahalarta sun yi musayar bayanai da kimantawa kan tattaunawar da aka yi a Alaska tsakanin shugabannin Amurka da Rasha, da kuma tattaunawar da aka yi a Washington tsakanin Shugaba Trump, Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy, shugabannin kasashen Turai da wakilan EU da NATO," in ji Yilmaz.

Ya jaddada cewa tattaunawa kai-tsaye tsakanin bangarorin a nan gaba na iya zama "sabon mataki" ga diflomasiyya.

Wannan shiri, wanda Birtaniya da Faransa ke jagoranta, yana da nufin tura sojojin kiyaye zaman lafiya daga kasashen Turai da NATO zuwa Ukraine bayan yakin ya kare.

Trump a ranar Litinin ya ce shugabannin sun tattauna kan tabbacin tsaro ga Ukraine, kuma gwamnatinsa ta fara shirin taron tsakanin Putin da Zelenskyy, sannan daga baya wani taron koli na uku da zai hada shi da su.

Taron da aka yi a Washington ya biyo bayan taron koli na Trump da Putin a jihar Alaska ta Amurka wanda aka shirya don kawo karshen yakin da ke Ukraine.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us