NIJERIYA
2 minti karatu
Babban Hafsan Tsaron Nijeriya ya kare yadda sojoji ke tunkarar masu tayar da ƙayar baya
Sojojin Nijeriya na ƙara amfani da hare-haren sama kan ƙarin barazanar ‘yan bindiga a yankunan arewaci da tsakiyar ƙasar.
Babban Hafsan Tsaron Nijeriya ya kare yadda sojoji ke tunkarar masu tayar da ƙayar baya
Babban hafsan tsaron Nijeriya, Christopher Musa / Reuters
2 awanni baya

Babban Hafsan Tsaron Nijeriya ya kare yadda jami’an tsaron ƙasar suke tunkarar masu tayar da ƙayar baya da masu aikata laifi lamarin da wasu lokuta kan janyo mutuwar fararen-hula, yana mai cewa rundunar sojin na iya ƙoƙarinta wajen kauce wa rasa rayuka.

Sojin Nijeriya na ƙara amfani da hare-haren sama kan masu ɗauke da makamai a yankunan arewaci da tsakiyar ƙasar.

Kazalika rundunar sojin ta amsa kai hare-hare kan fararen-hula yayin fatattakar gungun ‘yan bindiga a arewa maso yammacin ƙasar, inda ake fama da rashin tsaro, kuma rundunar sojin ta yi alƙawarin gudanar da bincike kan waɗannan kura-kuran.

Babban Hafsa Tsaro, Janar Christopher Musa, ya kuma yi kira da a gyara dokokin ƙasa da ƙasa, yana mai cewa dokokin na takura wa dakarun ƙasar yayin da suka ƙyale ‘yan bindiga suna “kisa yadda suke so.”

A wata tattaunawa da bai saba yi wa manema labarai ba a babban birnin ƙasar Abuja ranar Laraba, Janar Musa ya ce rundunar sojin na yawan dakatar da ayyukanta domin hana cutar da fararen-hula, ko da ma yin hakan zai sa ta rasa damar da take da ita a fagen daga.

"Ana bayyana mu a matsayin waɗanda suke aikata zalunci mafi muni, amma zan iya tabbatar maka da cewa muna yin iya ƙoƙarinmu. Muna mutunta ‘yancin ɗan’adam kuma muna martaba rayukan fararen-hula," kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambato shi.

"Muna yawan fasa ayyuka domin kauce wa rasa rayukan fararen-hula... wannan, a wasu lokutan, yakan tsawaita rikici."

Kamalan na zuwa ne yayin da ake yin ƙarin bincike kan yaƙin da ake yi da masu tayar da ƙayar baya a Nijeriya da kuma zarge-zargen da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama ke yi da ke cewa sojoji na yin amfani da ƙarfi fiye da ƙima.

Janar ɗin sojin ya yi ishara ga horarwar da ake yi wa dakarunsu kan ‘yancin bil’adama da kuma dokar ‘yancin ɗan’adam na ƙasa da ƙasa, a matsayin wata hujja ta ci-gaba.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us