SIYASA
3 minti karatu
Shin ya dace INEC ta yi wa ƙarin jam'iyyu 171 rajista a Nijeriya?
Farfesa Kamilu Sani Fagge na tsangayar nazarin siyasa a Jami’ar Bayero ta Kano ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa akwai alfanu da rashin alfanun jam’iyyu barkatai a siyasar ƙasa.
Shin ya dace INEC ta yi wa ƙarin jam'iyyu 171 rajista a Nijeriya?
INEC / TRT Afrika Hausa
3 awanni baya

Masana harkokin siyasa a Nijeriya sun fara tofa albarkacin bakinsu dangane da dacewa ko rashin dacewa bayan wasu sabbin jam’iyyu guda 171 sun gabatar da bukatar neman a yi musu rajista a Hukumar Zabe ta Kasar (INEC).

Wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Ilmantar da Masu Kada Kuri’a na INEC, Sam Olumekun ya fitar ta ce an wallafa duka sunayen sabbin jam’iyyu da suke neman rajista a shafin intanet din hukumar.

Ya ce zuwa ranar Laraba 3 ga watan Satumban bana, akwai jimillar jam’iyyu 171 da suke neman rajista.

Farfesa Kamilu Sani Fagge na tsangayar nazarin siyasa a Jami’ar Bayero ta Kano ya shaida wa TRT Afrika cewa akwai alfanu da rashin alfanun jam’iyyu barkatai a siyasar ƙasa.

Ya ce wadanan kungiyoyi da suke neman a yi musu rajista suna da ’yancin neman hakan a doka. 

Malamin jami’ar ya ce bayar da dama a samu jam’iyyu da yawa yana bai wa jama’a damar tsayawa takara kuma a ɗaya ɓangaren yana ba su damar zabar ’yan takarar da suke so.

Ko da yake wasu masana suna ganin hakan yana tattare da wasu ƙalubale saboda suna cewa hatta wajen gudanar zabe kudin da za a kashe zai yi yawa sosai saboda yawan jam’iyyu musamman ta fuskar ƙara yawan kayayyakin zaɓen da za a buƙata.

Idan za a tuna a shekarar 2020, hukumar zaben kasar ta soke rajistar wasu jam’iyyu 74 saboda ko dai sun kasa cin ko da kujera daya a shekarar 2019, ko kuma ba su cike wasu tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Nijeriya ba.

Sakamakon haka ne ya sa jam’iyyu 18 kawai suka iya fafatawa a zaben shekarar 2023.

Farfesa Kamilu ya ce idan jam’iyyu suka kai har guda 171, to gaskiya za a samu galibin jam’iyyun na je-ka-na-yi-ka ne.

Ya ce ko yanzu haka akwai jam’iyyu da dama a Nijeriya, amma guda hudu kaɗai ake jin ɗuriyarsu.

Ya ce wani ƙarin ƙalubale da yawan jam’iyyu barkatai zai jawo shi ne ruɗa masu kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓe musamman waɗanda ba su iya karatu ba.

Sannan masanin ya ce hatta bayan zaɓe ana iya samun ƙalubale daga wasu ƙananan jam’iyyu, ya ce za ka ga wata ƙaramar jam’iyya ko kujerar kansila ba ta ci ba, amma kuma sai ta garzaya kotu tana zargin an yi mata maguɗi.

Malamin jami’ar ya ce sakamakon haka sai a kwashe tsawon lokaci da kuɗi ana shari’a babu gaira babu dalili.

Sakamakon haka ya ce duk da kungiyoyin da ke neman zama jam’iyyu suna da ’yanci yin haka, amma ya kamata a riƙa bin tsari da ƙa’ida.

Ya bayar da misalin lokacin da aka yi irin haka a jamhuriya ta biyu a Nijeriya.

Ya ce abin da ya faru shi ne duk wata jam’iyya da aka yi wa rijista tana da damar shiga zabe, amma kafin ta shiga zabe akwai sharadin cewa sai ta ajiye wasu makuɗan kuɗi, wadanda idan ta ci wani kaso na ƙuri’u sai hukumar zabe ta dawo mata da kudinta.

Idan kuma ba ta ci kason da aka ƙayyade na ƙuri’u ba, to shi ke nan ta yi asarar kudinta.

Farfesa Kamilu ya ce idan aka yi wani abu mai kama da wannan, to hakan zai taimaka wajen rage jam’iyyu barkatai kuma hakan zai samar da tsari da tsafta.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us