Wata sabuwar taƙaddama ta ɓarke tsakanin jam’iyyar APC da kuma jam’iyyun adawa a Nijeriya kan batun ikirarin da Shugaba Bola Tinubu ya yi cewa kasar ta riga ta samu kuɗaɗen shiga da yawa a bana har ma ya zarta abin da ake zaton samu duk da cewa saura watanni uku kafin shekarar 2025 ta ƙare.
Yayin da APC ta kafe cewa Shugaba Tinubu ya ɗora Nijeriya kan alƙiblar bunkasar tattalin arziki, jam’iyyun adawa kamar ADC da NNPP da kuma LP su kuma sukar Shugaban Ƙasar suke yi cewa yana farin ciki da alƙaluman ci-gaban da aka samu ta fuskar kuɗaɗen shiga a daidai lokacin da ’yan ƙasa suke cikin matsin tattalin arziki.
Nijeriya ta kwashe tsawon shekaru tana dogaro da man fetur wanda yake bai wa gwamnati kaso 70 cikin 100 na kuɗaɗen shiga.
Gwamnatocin baya sun sha yin alkawarin cewa za su ƙirƙiro wasu hanyoyin samun kuɗaɗen shiga don bunƙasa tattalin arziki, sai dai duk da haka man fetur ya ci gaba da kasancewa babbar hanyar samun kuɗaɗen shigar gwamnati.
A shekarar 2023 lokacin da Shugaba Tinubu ya hau karagar mulki ya ƙaddamar da sauye-sauyen tattalin arziki da dama da niyyar bunƙasa tattalin arzikin kasar.
Cikin manyan matakan da Tinubun ya fara dauka har da cire tallafin man fetur da karya darajar naira da sauransu.
Ko da yake kimanin shekaru biyu bayan ɗaukar matakan, wasu masana suna sukar tsarin nasa, inda suke alaƙanta hakan da matsanancin halin da ’yan kasar suke ciki na talauci da hauhawar farashin kayayyaki da kuma tsadar rayuwa da sauransu.
Amma a ɗaya ɓangaren gwamnati ta samu ƙarin kuɗin shiga, kuma su ma gwamnatocin jihohi sun samu ƙarin kuɗaɗen da gwamnatin tarayya take ba su duk wata, sai dai ’yan kasar da dama suna ganin har yanzu ba su fara jin tasirin wannan ci-gaba da gwamnati ta ce an samu ba.
Shugaba Tinubu ya ce yanzu tattalin arzikin kasar ya daidaita. An samu daidaito ta fuskar musayar kuɗaɗen ƙasashen waje. Yanzu ana iya yin hasashe kan tattalin arziki.
Sannan ya ce ba ka bukatar sanin Gwamnan Babban Bankin Kasar (CBN) Yemi Cardoso kafin ka shigo da kaya daga waje ko kuma ka samu kuɗaɗen kasashen waje, kamar yadda Mai Magana da Yawun Shugaban Nijeriya Bayo Onanuga ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.
Tinubu ya ce kuɗin da Nijeriya ta samu daga ɓangaren da ba na man fetur ba ya kai naira tiriliyan 20.59, wanda a cewarsa hakan ya zarta abin da aka samu a bara inda ƙasar ta samu naira tiriliyan 14.6.
To amma masana tattalin arziki kamar irin su Dokta Usman Bello, Malami a fannin tattalin arziki a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa babu abin alfahari ga waɗannan ci-gaba da Shugaban Ƙasa ya ce an samu.
Ya ce saboda kuɗaɗen da Tinubun yake murnar samunsu, an samo su ne ta hanyar karbar haraji daga wajen ’yan ƙasa da kamfanoni da masana’antu wanda a cewarsa sanin kowa ne ƙarin haraji ga masana’antun da ke samar da kayayyakin yau da kullum yana cikin dalilan da suke jawo hauhawar farashin kayayyaki a ƙasa.
Masanin tattalin arziki ya ce idan gwamnati tana so talakawa su riƙa amfana da irin wannan ci-gaba, to dole ne ta duba wani abu guda da talaka yake matuƙar buƙatarsa amma kuma yana neman gagararsa, sai ta yi masa tallafi, ko da ba kai-tsaye ba.
Dokta Usman ya ce ko da a ce gwamnati ba za ta dawo da tallafin mai ba, to ya kamata ta yi wa man dizal tallafi saboda shi ne man da manyan motoci suke amfani shi.
A ganinsa da zarar an yi hakan za a ga farashin kayayyakin masarufi sun fara sauka kuma sakamakon hakan talaka zai samu sauƙin rayuwa.