NIJERIYA
1 minti karatu
Sojojin Nijeriya sun ceto mutum 76 da aka sace a Jihar Katsina
Sojojin Saman Nijeriya ne suka samu wannan nasara a yankin Karamar Hukumar Kankara yayin wani aiki na yunkurin kamo wani shugaban 'yan bindiga mai suna Babaro, wanda ake zargi da hannu a wani mummunan hari kan masallata a makon da ya gabata.
Sojojin Nijeriya sun ceto mutum 76 da aka sace a Jihar Katsina
Rundunar Sojin Sama ba ta bayar da amsa kai tsaye ga kira ko sakonnin da aka aika don neman karin bayani ba. / AP
24 Agusta 2025

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta ceto mutum 76 da aka yi garkuwa da su, ciki har da mata da yara, bayan wani hari ta sama da sojojin suka kai kan maɓoyar 'yan bindiga a Jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Nijeriya, kamar yadda mahukunta suka bayyana a ranar Asabar.

Harin wanda aka kai a Tsaunin Pauwa da ke yankin Karamar Hukumar Kankara, na daga cikin yunkurin na kamo wani shugaban 'yan bindiga mai suna Babaro, wanda ake zargi da hannu a wani mummunan hari da aka kai kan masallata a makon da ya gabata a garin Malumfashi da ke arewa maso yammacin Nijeriya.

Wani yaro ya rasa ransa yayin aikin ceton, kamar yadda ma'aikatar tsaron cikin gida ta jihar ta bayyana, amma ba a tabbatar da ko akwai wasu waɗanda suka jikkata daga cikin waɗanda aka ceto ko kuma daga cikin 'yan bindigar ba.

Rundunar Sojin Sama ba ta bayar da amsa kai tsaye ga kira ko sakonnin da aka aika don neman karin bayani ba.

Wannan harin ta sama na iya zama wani muhimmin ci gaba a kokarin rusa kungiyoyin masu aikata laifuka a arewa maso yammacin Nijeriya, inda 'yan bindiga ke addabar al'ummomin karkara tsawon shekaru.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us