RAYUWA
2 minti karatu
Hilda Baci: Fitacciyar mai girki ta Nijeriya ta dafa buhu 200 na shinkafa a yunƙurin kafa tarihi
A shekarar 2023 Hilda ta shiga kundin bajinta na Guiness World Record bayan shafe awa 93 da mintuna 11 tana girki.
Hilda Baci: Fitacciyar mai girki ta Nijeriya ta dafa buhu 200 na shinkafa a yunƙurin kafa tarihi
Kafin a tabbatar da cewa ta kafa tarihi, har sai kundin Guinness World Record ya tantance girkin da ta yi. / Reuters
15 awanni baya

Fitacciyar mai girkin nan Hilda Effiong Bassey, wadda aka fi sani da Hilda Baci, ta kammala yunƙurinta na sake kafa tarihi a duniya ta hanyar girka tukunyar dafa-dukar shinkafa mafi girma bayan shafe awa takwas tana girkin.

A shekarar 2023 Hilda ta shiga kundin bajinta na Guiness World Record bayan shafe awa 93 da mintuna 11 tana girki.

A wannan karon, Hilda ta girka ƙananan buhuna 200 na shinkafa wanda nauyinsu ya kai kilo 4,000 da katan 500 na tumatir da kilo 600 na albasa da sauran kayan haɗi.

An gudanar da zaman girkin a fili a cikin birnin kasuwanci na Legas, lamarin da ya ja hankalin ɗaruruwan masu kallo.

Kafin a tabbatar da cewa ta kafa tarihi, har sai kundin Guinness World Record ya tantance girkin da ta yi.

Jollof rice ko kuma dafa-dukar shinkafa abinci ne da ake sha'awa sosai a yankin Yammacin Afirka, inda ƙasashe kamar Nijeriya, Ghana, Senegal, Kamaru, da Gambiya ke da'awar cewa su ne ke da mafi kwarewa a wurin girka ta.

A shekarar 2023, Hukumar Ilimi, Kimiyya, da Al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta amince da Senegal a matsayin wurin da wannan abinci na dafa-dukar shinkafa ta samo asali.

Ana ammanar cewa abincin ya samo asali ne daga jama’ar Wolof na Senegal.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us