Ana zargin dakarun RSF na Sudan da buɗe wuta kan wani asibiti a birnin El-Fasher na jihar Darfur ta Arewa, tare da yin garkuwa da mata shida da yara biyu daga sansanin 'yan gudun hijira, kamar yadda masu ceto da wani likita suka bayyana a ranar Lahadi.
El-Fasher, wanda RSF ta yi wa ƙawanya fiye da shekara guda, shi ne birni mafi girma a yammacin Darfur da ke hannun sojojin gwamnati, kuma yana ɗaya daga cikin wuraren da ake rikici tun bayan ɓarkewar yaki a watan Afrilun 2023.
A ranar Lahadi, ɗakin bayar da agajin gaggawa na sansanin Abu Shouk da ke kusa da El-Fasher ya bayyana cewa, mayakan RSF sun kutsa cikin sansanin, inda suka kama fararen hula takwas – mata shida, jariri mai kwanaki 40 da wani yaro dan shekara uku – suka tafi da su zuwa wani wuri da ba a bayyana ba. Har yanzu RSF ba ta mayar da martani kan rahotannin ba.
Masu ceto sun ce fiye da mutum 20 daga sansanin sun ɓace, inda suke gargaɗin cewa adadin na iya fin haka.
Harba makaman atilari kan asibit
Sansanin Abu Shouk, wanda ke ɗauke da dubban 'yan gudun hijira, an kai masa hari sau biyu a wannan watan. Harin farko ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 40, a cewar masu bayar da agaji na farko.
A ranar Asabar, makaman da RSF suka harba sun samu sashen kula da marasa lafiya da ke buƙatar agajin gaggawa na wani asibiti a El-Fasher, inda ya jikkata mutane bakwai, ciki har da wani ma’aikaci, kamar yadda wani likita ya shaida wa AFP.
Harba makaman, wanda ya ci gaba har zuwa safiyar Lahadi, "ya lalata sashen gaggawa, wanda ya sa dole mu dakatar da ayyukanmu," in ji likitan, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro.
Asibitin yana daya daga cikin asibitoci uku da ke ci gaba da aiki a birnin.
Yunwa
Tun bayan da RSF ta rasa birnin Khartoum a watan Maris, ta kara kai hare-hare kan El-Fasher da sansanoni da ke kewaye da shi domin karfafa ikon ta a yammacin Sudan.
Abu Shouk yana daya daga cikin sansanoni uku da ke wajen El-Fasher inda aka ayyana cewa ana fama da yunwa a karshen shekarar 2024.
Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi cewa yunwa na iya bazuwa zuwa birnin, duk da cewa rashin bayanai ya jinkirta yiwuwar ayyana hakan.
Rikicin, wanda ya kashe dubban mutane, ya haifar da abin da Majalisar Dinkin Duniya ta kira babbar matsalar gudun hijira da yunwa a duniya.