NIJERIYA
2 minti karatu
An gurfanar da mutum biyar a kotun Abuja kan kisan da aka yi a Cocin Katolika a Owo da ke Ondo
Ana tsammanin sharia’ar za ta zama zakaran gwajin dafin ikon gwamantin Nijeriya na iya hukunta batutuwa da suka shafi aikata ta’addanci a shari’ance, yayin da ƙasar ke fama da masu tayar da ƙayar baya da rashin tsaro.
An gurfanar da mutum biyar a kotun Abuja kan kisan da aka yi a Cocin Katolika a Owo da ke Ondo
An kashe mutane da dama a harin Cocin Owo a Jihar Ondo / Reuters
12 Agusta 2025

Masu gabatar da ƙara a Nijeriya sun gurfanar da mutum biyar da ake zargi da kitsa harin da wasu masu iƙirarin jihadi suka kai a wani Cocin Katolika a garin Owo, na Jihar Ondo da ke kudu maso yammacin ƙasar inda suka kashe mutum 50 tare da jikkata fiye da mutum 100 a shekarar 2022.

Waɗanda ake tuhumar - Idris Omeiza, Al Qasim Idris, Jamiu Abdulmalik, Abdulhaleem Idris and Momoh Otuho Abubakar – sun gurfana a gaban wata kotun gwamnatin taraya a Abuja, inda aka gurfanar da su bisa dokar hana ta’addancin Nijeriya.

Waɗanda ake zargin sun ce ba su aikata laifukan da ake zarginsu da yi ba, kuma an ajiye su a hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).

Alƙali Emeka Nwite ya ɗage zaman kotun zuwa ranar 19 ga watan Agusta.

Ana tsammanin sharia’ar za ta zama zakaran gwajin dafin ikon gwamantin Nijeriya na iya hukunta batutuwa da suka shafi aikata ta’addanci a shari’ance, yayin da ƙasar ke fama da masu tayar da ƙayar baya da rashin tsaro.

Takardun ƙara da aka shigar a kotun sun yi zargin cewa mutanen sun shiga ƙungiyar ta’addancin gabashin Afirka Al Shabaab a shekarar 2021 kuma sun kitsa kai hari a wata makarantar gwamnati a tsakiyar Nijeriya da kuma kusa da wani masallacin da ke da nisan kilomita 30 daga cocin St Francis na ɗarikar Katolika a garin Owo.

Al Shabaab ba ta  ɗauki alhaƙin kai harin na watan Yunin shekarar 2022 ba, kuma kawo yanzu babu tabbacin cewa tana aika-aika a cikin Nijeriya.

Daga farko dai hukumomi sun ɗora alhakin kai harin kan ƙungiyar ISWAP, wadda, tare da Boko Haram ta shafe shekaru tana ƙaddamar da hare-hare kan yankin arewa maso gabashin Nijeriya, duk da cewa ƙungiyar ma ba ta ɗauki alhakin kai hare-haren ba.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us