Abel Kai mutum ne mai tsayin ƙafa shida, kuma yana da zubin jiki mai diri, da kwarjini wajen tafiya, da yawan murmushi. Abel ya saba jan hankali duk inda ya je.
Ba ka sanin lalurar Abel sai ya yi magana, abin da ke hana shi ƙulla tunaninsa cikin kalamansa sakamakon matsananciyar in’ina.
Matsayin Abel tauraro ne wanda ake nema don tallata kayan ƙawa a kenya. Aikinsa ya mayar da shi jakada kan ɗaukaka darajar masu in’ina da kuma lalurar magana.
Abel wanda aka haifa a tuddan wajen birnin Nairobi a 1996 ya faɗa wa TRT Afrika cewa, "Ina firamare, an nemi na karanta wani sakin layi. Na yi fama da furta haruffa".
"In’inata ta tsananta bayan wannan lokacin, kuma na yi ta fama da damuwa da shan wahala. Ina in’ina sosai har nakan fashe da kuka."
Abokan karatunsa suna zargin in’inarsa tana iya yaɗuwa. Hoto: Abel Kai
In’ina larurar furucice da ke shafar iya magana, kuma take janyo tirjiyar furuci. Wannan cikas yana iya janyo maimaita furuci, tsawaitar shiru, da kasa magana ko furta wasu kalmomi.
A wajen Abel, lokacin yana yaro mai neman shiga cikin sa’o’insa, ya sha wahala wajen amsar yanayin da yake fama da shi na in’ina, a duk sanda zai yi magana.
Mafi munin lamarin shi ne idan ya kalli fsukar abokansa duk sanda yake yin in’ina.
Abel ya ce, "‘Yan ajinmu sukan guje mini, saboda yana tunanin in’ina tana yaɗuwa. Na so kare kaina, don bayyana cewa ba lalura ce mai yaɗuwa ba balle su iya ɗauka, amma duk sanda na yi ƙoƙarin magana sai wata in’inar ta cim mani".
Abubuwan da ke janyowa
Duk da ba a gane musabbabin in’ina ba, an yi imanin cewa tana faruwa ne daga tsatso, da kuma dalilan halittar jijiya da na mazauni.
Har yanzu matsalar lafiyar tana ɗaure wa ma’aikatan lafiya kai, saboda babu fayyaceccen bayani kan yadda ake magance ta, duk da masu jiyyar lalurar furuci suna taimaka wa kan matsalar cikin tsawon lokaci.
Akwai wasu lokutan da in’ina mai jan lokaci takan tafi da kanta, bayan mai ita ya kai wasu shekaru.
Abel ya yi amanna cewa cewa rashin ilimi kan lalurar wani ɓangare ne na matsalar. Ya ce mutane sukan lura da mai in’ina amma ba su faye fahimtar nauyin da laulurar ke zuwa da shi ba.
Ya bayyana cewa, "In’ina ɓangare ne ƙarami na babbar matsala. Babban ƙalubalen shi ne yakan ɓuya daga idon mutane. Baya ga matsalar furuci da ake iya gani, a baɗni mutum kan shiga ƙangin rashin yarda da kai, da ƙyama da karya ƙarfin zuciya".
Saboda haka, shin zamantowa tauraro da ke tallata kayan ƙawa yana taimakawa wajen rage munin da kuma mummunan kallon da mai 'in’ina ke samu.
"Lokacin da na girma, na gane cewa in’inar da nake yi ba abu ne da zan yi fata ba - wani bangaren halittata ce, maimakon in dage sai na daina. Na zabi na rungume shi," Abel ya shaida wa TRT Afrika.
"Wannan karbuwa ba abu ne mai sauki ba, amma ya koya mani juriya da wayewar kai. Na koyi tafiyar da al'amuran zamantakewa daban-daban, na shirya kaina cikin tunani don tattaunawa da kuma samar da dabarun ci gaba da kasancewa."
Rashin yarda da kai
Bayan abin da ya shafi jiki, yin in’ina na iya yin tasiri ga ƙima da mu'amalar mutum.
Wannan shi ne duk da tabbacin kimiyya cewa akasin rashin fahimta na yau da kullum, in’inaba ta da alaka da basira ko jin tsoro.
Abel ya ce: “Bacin rai na ƙoƙarin faɗin sunana, wulakanci da ake yi min sa’ad da nake makaranta, da kuma tsoron yin magana a bainar jama’a a kai a kai shi ne damuwar da na yi ta fama da ita. Amma ban bar hakan ya daƙushe ni ba. Na kammala karatuna ta hanyar zama wanda ya fi kowa a ajinmu a fannin kayan ƙawa,” in ji Abel.
Mai tallar kayan ƙawar na Kenya ya bayyana cewa babban ƙalubalensa shi ne yadda in’inar ke shafar walwalarsa.
“Takaici da fargaba suna ƙara ta’azzara lamarin,” in ji Abel. Idan ina jin tsoro ko tashin hankali, in’inar ta fi ƙamari, lamarin da ke sa na kasa magana da kyau. A hankali, sai na koya wa kaina nutsuwa da kwantar da hankali saboda in ba haka bahakan na shafar mu’amalata da mutane.
Idan aka kwatanta da shekara 20 da suka gaba, mutane da dama a yau sun san yadda mai in’ina ke ji da azabtuwar da yake yi idan ya gaza bayyana kansa. Abel ya ce haka ya yi ta fama ta hanyar fafutuka da wayar da kai don ya samu mutane masu taya shi yaɗa saƙon daina ƙyamar mau in’ina.