Daga Pauline Odhiambo
Har yanzu Michael Otieno yana tunawa da bulalar da aka yi masa. Ba kawai a hannunsa ba, amma a tunanin kansa.
A makarantarsa ta firamare da ke yammacin Kenya, bulala ta zama ruwan dare kamar yadda allo ya zama.
"Idan ka makara, sai an yi maka bulala. Idan kuka manta aikinku na gida, sai a yi muku bulala.
“Ba batun koyarwa ba ne, ya zama sanya tsoro ne kawai," in ji wani akawu mai shekaru 32 mazaunin birnin Nairobi yayin tattauna wa da TRT Afrika.
"Wannan tsoron bai sa na zama dalibin da ya fi saura ba, ya sanya ni cikin damuwa, ya sa na yi imani cewa tashin hankali shi ne maganin farko na wata matsala. Ya ɗauke ni shekaru da yawa kafin na watsar da wannan ra’ayin."
Ba Otieno ne kaɗai ke dauke da tabon hukunci da bulala ba har zuwa lokacin da ya girma. A cewar wani sabon rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) mai taken - "Hukunta Yara: Tasirin Kiwon Lafiyar Jama'a" - azabtarwa ta jiki da sunan gyara yara ya zama ruwan dare gama gari kuma yana haifar da lahani mai ɗorewa ga lafiyarsu da ci gabansu.
Matsala gama-gari
Binciken ya nuna cewa kimanin yara biliyan 1.2 a fadin duniya suna fuskantar azabtarwa ta jiki a gida kowace shekara.
Kasashen Afirka ba a bar su a baya ba, yayin da iyaye suka bayar da rahoton cewa kashi 77% na yara a Togo da kashi 64% a Saliyo masu shekaru 2-14 na fuskantar hukunci a makarantu, kuma sakamakon ya samu ne wata guda kafin fitar da wannan rahoto.
Makarantu ma ba su fita daga wannan koma ba. Binciken ya nuna cewa kashi 70 cikin 100 na yara a fadin Afirka na fuskantar bulala a lokacin karatunsu na makaranta.
Etienne Krug, daraktan sashen tantance lafiya na WHO ya ce "Yanzu akwai kwararan shaidun kimiyya da suka nuna cewa hukunta yara na haifar da hatsari da yawa ga lafiyar yaran."
"Ba ya bayar da wata fa'ida ga halayya, ci gaba ko kyautata rayuwar yara, kuma ba wani amfani ga iyaye ko al'umma. Lokaci ya yi da za a kawo karshen wannan mummunar dabi'a."
Illa mai dawwamammiya
Rahoton na WHO ya yi cikakken bayani game da yadda yi wa yara bulala ko wani nau’in hukunci da ya shafi jiki ke haifar da cutar wa ga lafiyarsu, ciki har da yawaitar damuwa ga kwayoyin halitta da sauyi kan yadda kwakwalwarsu ke aiki.
Akwai shaida ta kimiyya da ke nuna cewa yaran da suka fuskanci irin wannan horon ba su da yiwuwar samun ci gaba da kashi 24% fiye da takwarorinsu waɗanda ba su fuskanci hakan ba.
Lamarin na shafar lafiyar kwakwalwa, tare da ƙarin hatsarin damuwa, tsananin damuwa da ƙarancin girmama kai waɗanda galibi suna dawwama har zuwa girma.
Ma’aikaciyar kula da yara Adeola Okonkwo, wacce ke aiki a Legas a Najeriya, tana shawartar iyaye akai-akai da su yi amfani da wasu hanyoyin da za su bi wajen ladabtarwa.
Okonkwo ta ce: “A koyaushe ana cece-kuce, ‘An yi min duka kuma na samu lafiya’. "Amma mun kasance?
Da yawa daga cikinmu suna ɗauke da raunukan ɓoye da ke nuna yadda muke saurin mayar da martani cikin fushi, rashin iya bayyana motsin zuciyarmu, da kuma zuzzurfar buƙatar aminta.
Muna cakuda girmama wa da tsoro. Muna karya ruhun 'ya'yanmu kuma muna kiran shi horo."
Rusa wannan ta’ada
Binciken na WHO ya tabbatar da abin da watakila ko da yaushe aka sani amma ba a kula da shi - cewa yaran da aka yi wa bulalar na zama manya da su ma suke yin hakan, suna mayar da illar ba komai ba.
Waɗannan yaran kuma an san su da nuna ɗabi'ar fada d abacin rai da yiwuwar yin tashin hankali ko aikata laifuka daga baya a rayuwarsu.
Duk da cewa da yawa daga cikin ƙasashen Afirka sun haramta ladabtar da yara a makarantu, binciken ya nuna cewa doka kawai ba ta isa ta kawar da imanin da ke da tushe ba game da yadda ya kamata a horar da yara a gida da kuma a aji.
WHO ta fayyace cewa dole ne a ƙara yin doka tare da gangamin wayar da kan jama'a da tallafin ƙwararru ga iyaye da malamai.
Ga mutane irin su Otieno, binciken ya zama ingantaccen abin da suka fuskanta amma sun sami wahalar bayyana halin da suka shiga saboda yanayin zamantakewa.
"Dole ne mu tambayi kanmu ainihin abin da muke koya wa yaranmu," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
"Shin muna koyar da su daidai ne ko kuskure, ko kuwa muna koya musu cewa karfi yana sanya wa a yi rigima?
Ƙawo karshen wannan ba wai rashin mutunta al'adunmu ba ne; yana nufin zabar makoma mai kyau, mafi tsafta ga al’ummu masu zuwa. Ilimin kimiyya ya bayyana a fili. Cutar da gaske ce. Yanzu ne lokacin kawar da matsalar."