DUNIYA
2 minti karatu
Austria za ta haramta wa ɗalibai 'yan ƙasa da shekaru 14 sa ɗankwali da hijabi
Duk wanda bai bi umarnin ba za a gana da iyayensa, kuma za a ci su tara daga $175 zuwa $1,170.
Austria za ta haramta wa ɗalibai 'yan ƙasa da shekaru 14 sa ɗankwali da hijabi
Masu zanga-zanga suna ɗauke da tutar nuna adawa da wariyar launin fata da manufar bautar 'yan gudun hijira ta Turai a birnin Vienna, Austria a ranar 18 ga Maris, 2017. / Reuters
10 awanni baya

Ministar Harkokin Hadin Kai da Kula da Iyali da Harkokin EU ta Austria, Claudia Plakolm, ta sanar a ranar Laraba cewa gwamnati ta amince da haramcin sanya hijabi ga yara 'yan kasa da shekaru 14 a makarantu.

Plakolm ta bayyana bayan taron majalisar ministoci cewa wannan dokar za ta fara aiki a lokacin kaka mai zuwa.

Ta jaddada cewa dokar za ta shafi makarantu na gwamnati da masu zaman kansu, tare da bayyana cewa rashin bin dokar zai kai ga kiran taro da iyaye, sannan a iya ƙaƙaba musu tara daga $175 (€150) zuwa $1,170 (€1,000).

Da aka tambaye ta dalilin da yasa dalibai za su iya sanya gicciye (kuros) amma ban da hijabi, sai Plakolm ta ce hijabi alama ce ta "zalunci."

Ta ce nauyin gwamnati ne ta tabbatar da cewa 'yan mata sun girma cikin 'yanci don su yanke shawara da kansu, tana mai jaddada cewa makarantu dole ne su zama wuraren da ba za a samu wani abu da zai hana ci gaba ba.

"'Yan mata su samu damar girma cikin 'yanci, a bayyane, da kuma cikakkiyar ƙwarin gwiwa a ƙasarmu," ta rubuta a wani sakon ta a X.

"Wannan shi ne dalilin da yasa muka yanke shawarar haramta hijabin yara. Za a hada wannan da wani shirin wayar da kai ga iyaye, da ƙarfafa 'yan mata, da kuma aiki kai-tsaye tare da samari," ta ƙara da rubutawa.

Kungiyar Addinin Musulunci a Austria (IGGO) ta soki wannan mataki, tana mai cewa duk kokarin da aka yi a baya don samun mafita ta tsarin mulki an yi watsi da su.

"Haramcin hijabi siyasa ce ta alama da ke cutar da yara da dimokuradiyya," in ji kungiyar a cikin wata sanarwa.

Ta yi gargadi cewa wannan matakin zai rage amincewa da bin doka kuma zai yi barazana ga hadin kan al'umma, tare da nuna wariya da ware yara maimakon karfafa su.

Kotun Tsarin Mulki ta Austria ta soke haramcin hijabi a shekarar 2020, saboda wani bangare na dalilin cewa ya fi karkata ga Musulmai.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us