Babban hafsan rundunar sojin Jamhuriyar Nijar (CEMA) Birgediya Janar Moussa Salaou Barmou ya jagoranci jana’izar sojojin ƙasar hudu da aka kashe a yayin wani hari da ‘yan ta’adda suka kai sansanin soji da ke Chetima Wango a daren Litinin 17 ga watan Maris na 2025.
Kamfanin dillancin labaran Nijar ya rawaito a ranar Talata cewa bayan da aka yi musu jana’iza ta addini sai kuma aka yi wa sojojin jana’izar ban-girma ta soji duk a Diffa.
Kazalika, Birgediya Janar Barmou ƙarƙashin rakiyar hafsan sojin ƙasa Kanal-Manjo Maman Sani Kiaou da mataimakin hafsan sojin sama Mr. Moctar Diallo da sauran manyan jami’ai sun ziyarci sojojin da suka ji raunuka waɗanda ke kwance a asibiti suna samun kulawa.
A ranar Litinin ne mayaƙan ISWAP suka ƙaddamar da wani mummunan hari a kan sansanin sojin da ke Chetima Wango a yankin Diffa, inda suka kashe sojoji huɗu tare da jikkata wasu da dama.
Maharan da ake kyautata zaton suna dauke da muggan makamai, sun nufi sansanin sojin ne a wani mataki na ci gaba da yaƙin da suke yi da jami'an tsaro a yankin.