GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Sojojin Isra'ila fiye da 1,500 sun nemi a kawo ƙarshen yaƙin Gaza
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi barazanar korar sojojin da suke aiki waɗanda suka yi kira a kawo ƙarshen yaƙin Tel Aviv.
Sojojin Isra'ila fiye da 1,500 sun nemi a kawo ƙarshen yaƙin Gaza
Nearly ten petitions have so far been issued by soldiers demanding an end to the Gaza war since Thursday. / Photo: Reuters
15 Afrilu 2025

Fiye da sojoji 1,500 na rundunar da ke kula da tankokin yaƙi ta Isra'ila, ciki har da janar-janar, sun sanya hannu kan wata takardar neman gwamnatin Isra'ila ta mayar da hankali kan dawo da waɗanda aka yi garkuwa da su a Gaza, ko da hakan zai kai ga dakatar da yaƙin da ake yi a yankin Falasdinawa.

A cewar Jaridar Maariv a ranar Litinin, sojoji 1,525 daga rundunar tankokin sun sanya hannu kan wannan takardar, daga masu ɗauke bindiga har zuwa janar-janar.

Sun bukaci gwamnati “ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da an sako wadanda aka yi garkuwa da su — ko da hakan zai kai ga dakatar da yakin.”

Waɗanda suka sanya hannun sun hada da sojojin da suka yi aiki a rundunar kula da tankoki sannan suka koma rayuwar farar hula ba tare da zuwa makarantar jami’ai ba da tsofaffin sojoji da ƙananan kwamandoji, da kuma tsofaffin manyan jami’an sojin Isra’ila, ciki har da tsoffin shugabannin rundunar tankoki da kwamandojin sassa, kamar yadda Maariv ta bayyana.

Sunayen masu sanya hannu sun hada da tsohon Firaminista kuma tsohon shugaban sojoji Ehud Barak da tsohon shugaban rundunar tsakiya Amram Mitzna da tsohon shugaban hafsoshin tsaro Dan Halutz da tsohon shugaban leƙen asiri na soja Amos Malka da tsohon shugaban rundunar tsakiya Avi Mizrahi, da kuma tsohon kwamandan rundunar tankoki ta 14 Amnon Reshef.

Wannan takardar buƙatar ta kasance wani bangare na wani babban kira daga sojoji na yanzu da tsoffin sojojin Isra’ila da ke neman a dawo da wadanda aka yi garkuwa da su tare da kawo karshen yakin.

Tun daga ranar Alhamis, an fitar da kusan takardu goma daga sojoji da ke neman a kawo karshen yakin Gaza.

Firaminista Benjamin Netanyahu ya yi barazanar korar sojojin da ke kan aiki wadanda suka sanya hannu kan wadannan takardu.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us