KASUWANCI
2 minti karatu
Google zai biya tarar dala miliyan 28 kan nuna wariyar launin fata
Karar da aka shigar ta ce ma'aikata Farar Fata da 'Yan Asia sun fi karbar albashi mai tsoka da samun damarmaki.
Google zai biya tarar dala miliyan 28 kan nuna wariyar launin fata
Google ya musanta aikata wani laifi amma ya ce sun cim ma matsaya. [REUTERS/Annegret Hilse]
19 Maris 2025

Google ya amince ya biya dala miliyan 28 saboda karar da aka kai kamfanin bisa zargin nuna wariyar launin fata wajen biyan albashi da damarmakin aiki, in ji BBC a ranar Laraba.

Karar da wata tsohuwar ma’aikaciyar Google, Ana Cantu ta shigar a gaban kotu a 2021, ta yi ikirarin cewa Hispaniyawa da Latino, ‘Yan Asalin Amurka da sauran ma’aikata tsiraru na karbar albashi kadan, kasa da na abokan aikinsu farar fata da ‘yan Asia.

Wasu takardu na kamfanin da suka fita ta bayan fage sun nuna bambancin kudaden sallama na matakin iri guda, wanda ke karfafa rashin daidaito in ji karar.

Biyan kudaden da ya shafi a kalla ma’aikata 6,632 da ke aiki a Google a tsakanin 15 ga Fabrairu da 31 ga Disamba, 2024, ya samu amincewar wani alkalin California.

Google ya musanta aikata wani laifi, amma ya ce sun cimma matsaya, in ji mai magana da yawon kamfanin, yana mai cewa Google zai biya ku

Lamarin na zuwa ne a lokacin da ake sauya salo a manufofin tsarin ayyuka, adalci da shigar da mutane (DEI. Google, Meta, Amazon, da sauran manyan kamfanoni sun rage aiki da hakan a ‘yan watannin nan, inda Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira da a kawar da tsarin a ayyukan gwamnati da ‘yan kwangila.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us