Shugaban Rundunar RSF ta Sudan ya ayyana kafa wata gwamnati a matsayin kishiya ga gwamnatin ƙasar da aka amince da ita a hukumance wadda ke tare da sojin ƙasar, yayin da sojin ƙasar suka yi shelar samun ƙarin nasarori a yammacin Omdurman.
Hakan na faruwa ne a yayin da aka cika shekaru uku ana gwabza yaƙi tsakanin ɓangarorin biyu.
"A wannan rana ta tunawa da fara yaƙin, muna alfaharin sanar da kafa gwamnatin zaman lafiya da haɗin kai, wata gamayya mai faɗi da ke nuna gaskiyar fuskar Sudan," in ji Mohamed Hamdan Daglo a wata sanarwa da ya fitar a manhajar Telegram ranar Talata.
Sai dai kuma, rundunar sojin Sudan ta bayyana cewa ta ƙara samun nasarori a yammacin Omdurman inda ta ƙwace wurare uku da kuma wani sansani daga hannun RSF.
A wata sanarwa, rundunar sojin Sudan ta yi iƙirarin cewa ta ci gaba da samun nasarori a yammacin Omdurman, tana mai cewa, "Dakarunmu a yau sun yi nasarar murƙushe mayaƙan RSF."
Ana kakkaɓe mayaƙan RSF daga garuruwan Al-Safwa da Al-Hilla Al-Jadida da ƙauyen Al-Safirah da kuma sansanin Konan, da kuma sauran ‘yan wurare da suka rage a yankin, in ji sojin.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa sojojin sun "lalata wasu motocin yaƙin RSF tare da kashe gomman mayaƙa kuma muna bin sauran da gudu."
Ana samun ƙarin kiran a kawo ƙarshen yaƙin
Wannan na faruwa ne yayin da ministocin harkokin wajen ƙasashen G7 masu ƙarfin tattalin arziƙi suka fitar da wata sanarwa ranar Talata suna masu kira da tsagaita wuta nan-take ba tare da wani sharaɗi ba, sannan suka yi Allah wadai da hare-haren RSF a Sudan.
Amurka ma ta yi Allah wadai "cikin kakkausar murya " da hare-haren runduar RSF a yammacin Sudan, tana nuna takaicinta kan yadda ake kai hare-hare a sansanonin ‘yan gudun hijira da kuma ‘yan ƙasa masu rauni.
A tsokacin da ta yi wa manema labarai, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Tammy Bruce ta ce RSF tana ƙaddamar da "hare-hare masu tsanani " kan babban birnin jihar Arewacin Darfur, El Fasher, da kuma sansanonin ‘yan gudun hijira da ke kusa da shi.
"Mun damu sosai game da rahotannin da ke cewa RSF ta kai wa fararen-hula hare-hare da masu ba da agajin jinƙai da gangan a Zamzam da Abu Shouk," in ji Bruce, tana ishara ga sansanonin.
Tun ranar 15 ga wata watan Afrilun shekarar, 2023, rundunar RSF ta fara yaƙi da sojin Sudan domin karɓe iko da ƙasar, lamarin da ya janyo dubban mace-mace da kuma bala’in jinƙai mafi muni a duniya.
Fiye da mutum 20,000 aka kashe yayin da aka raba mutum miliyan 15 da muhallansu, in ji MDD da hukumomi na cikin gida.
Bincike daga masana a Amurka kuwa ya nuna cewa yawan waɗanda aka kashe ya kai 130,000.
A cikin ‘yan makonnin nan, rundunar RSF ta rasa muhimman wurare a faɗin Sudan inda dakarun gwamnati ke ƙwace su.