NIJERIYA
2 minti karatu
Gwamnatin Nijeriya da Majalisar Dokoki sun goyi bayan tsarin mai da rubuta jarabawar WAEC ta komfuta
Wannan babban sauyin, wanda aka tsara cewa zai fara aiki a shekarar 2026 ya jawo mabambantan ra’ayoyi a tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin ilimi.
Gwamnatin Nijeriya da Majalisar Dokoki sun goyi bayan tsarin mai da rubuta jarabawar WAEC ta komfuta
Ministan Ilimi Maruf Alausa ya ce jarabawa ta tsarin CBT za ta ƙarfafa tsarin ilimin ƙasar / Others
3 Satumba 2025

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da Majalisar Dokokin Ƙasar sun nuna goyon bayansu kan mayar da rubuta jarabawar kammala sakandare ta Yammacin Afirka, WAEC da komfuta wato CBT.

Wannan babban sauyin, wanda aka tsara cewa zai fara aiki a shekarar 2026 ya jawo mabambantan ra’ayoyi a tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin ilimi.

Amma a yayin da yake jawabi a gaban Majalisar Dokoki da manyan masu ruwa da tsaki a wani taron wayar da kai a Abuja, Ministan Ilimi, Maruf Alausa ya ce jarabawa ta tsarin CBT da za a dinga yi a duka faɗin ƙasar, zai ƙarfafa tsarin ilimin ƙasar.

Alausa ya ce Gwamnatin Tarayya tana goyon bayan rubuta jarabawar WAEC ta komfuta saboda a kawar da satar amsa da kuma tabbatar da an yi sahihiyar jarabawa.

“Mun ɗau aniyar mayar da rubuta jarabawa ta tsarin fasahar komfuta a matsayin wani mataki na samar wa fannin ilimi martaba. A yayin da da fari wasu suka soki wannan sauyi, mun san cewa ba zai yiwu a ci gaba da bin tsarin da aka saba da shi ba.” in ji Minista Alausa.

“An yi wannan tsari ne rubuta jarabawa ta komfuta saboda a rage satar amsa da kare martabar jarabawowinmu. Hakan zai ƙarfafa darajar jarabawowinmu a cikin gida da ma ƙasashen waje.

A nasa bangaren, Shugaban Ofishin WAEC na Ƙasa, Amos Dangut ya ce an samu nasara a wannan sabon sauyin wanda aka fara gwajinsa a kan ɗalibai masu rubuta jarabawar WAEC ta kuɗi mai zaman kanta a shekarar 2024, kuma za a ƙara bunƙasa shi a faɗin kasar.

Dangut ya bayyana cewa, za a ɓullo da tsarin yin gwaji da koya wa ɗalibai yadda tsarin yake don taimaka musu wajen fahimtarsa sosai, yana mai jaddada cewa babu wani dalibi da za a bari baya.

Dangane da abubuwan da suka shafi samar da kayan aiki da matsalolin intanet, ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa WAEC ta yi nasarar gudanar da jarrabawar a wuraren da ke da wahalar isa ba tare da an samu cikas ba.

Ya ƙara da cewa zuwa yanzu sakamakon ɗaliban da suka rubuta jarabawar gwajin ta komfuta ya yi kyau sosai fiye da jarabawar takarda da aka saba rubutawa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us