NIJERIYA
2 minti karatu
DSS ta gurfanar da shugabannin Ansaru da ‘ke da alaƙa da fasa gidan yarin Kuje’ da laifin ta'addanci
A cewar hukumar ta sirri, laifukan da ake tuhumar su da su sun hada da jagorantar kungiyar ta’addanci, ba da kudaden gudanar da ayyukanta, da daukar ma’aikata, da kuma shirya ayyukan tarzoma a fadin kasar.
DSS ta gurfanar da shugabannin Ansaru da ‘ke da alaƙa da fasa gidan yarin Kuje’ da laifin ta'addanci
DSS Nigeria / Others
8 awanni baya

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta gurfanar da wasu manyan kwamandojin kungiyar Ansaru biyu, wata kungiyar ta’addanci da aka ce suna da alaƙa da Al-Qaeda, kan zarginsu da hannu wajen kai munanan hare-hare a Nijeriya.

Wadanda ake zargin su ne Mahmud Usman, wanda aka fi sani da Abu Bara’a Abbas/Mukhtar, wanda aka bayyana a matsayin Sarkin Ansaru, da mataimakinsa, Mahmud Al-Nigeri, wanda aka fi sani da Malam Mamuda.

An kama su ne a kwanan nan a yayin gudanar da ayyukan tsaro.

A cewar hukumar ta sirri, laifukan da ake tuhumar su da su sun hada da jagorantar kungiyar ta’addanci, ba da kudaden gudanar da ayyukanta, da daukar ma’aikata, da kuma shirya ayyukan tarzoma a fadin kasar.

Ana zargin mutanen biyu da hannu a harin da aka kai gidan yarin Kuje a watan Yulin 2022, inda fursunoni fiye da 600 da suka hada da wadanda ake zargi da Boko Haram suka tsere.

Ana sa ran gurfanar da wadanda ake zargin a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja nan ba da jimawa ba a cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Ƙasar.

Gurfanar da su gaban kotun na zuwa ne makonni uku bayan Mai Bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya sanar da kama su.

Ribadu ya bayyana cewa, “Na farko shi ne Mahmud Muhammad Usman (wanda aka fi sani da Abu Bara’a/Abbas/Mukhtar), wanda yake kiran kansa Sarkin ANSARU, shi ne kodinetan kungiyoyin ‘yan ta’adda daban-daban a fadin Nijeriya, kuma shi ne ya shirya wasu manyan sace-sacen mutane da fashi da makami da aka yi amfani da su wajen daukar nauyin ta’addanci tsawon shekaru.
“Na biyu shi ne Mahmud al-Nigeri (wanda aka fi sani da Mallam Mamuda), Abu Bara’s wanda aka ayyana shugaban ma’aikata kuma mataimakinsa, shi ne shugaban kungiyar da ake kira “Mahmudawa” da ke boye a ciki da wajen dajin Kainji, wanda ya ratsa jihohin Neja da Kwara har zuwa Jamhuriyar Benin.

"Mamuda ya samu horo a Libya tsakanin 2013 da 2015 a karkashin masu ikirarin jihadi na kasashen waje daga Masar, Tunisiya, da Aljeriya, inda ya ƙware kan sarrafa makamai da ƙirƙira IED."

Ribadu ya ce mutanen biyu sun kasance cikin jerin sunayen ‘yan Nijeriya da aka fi nema ruwa a jallo tsawon shekaru, inda suka jagoranci kai hare-hare da dama kan fararen hula, jami’an tsaro, da muhimman ababen more rayuwa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us