'Cutar sikilar da nake fama da ita ta sa na ji tsoron ba zan rayu na ga jaririna ba’
'Cutar sikilar da nake fama da ita ta sa na ji tsoron ba zan rayu na ga jaririna ba’
Sabbin dokokin WHO na kawar da gibin kula da lafiyar masu juna biyu da ke fama da cutar sikila, suna maye gurbin tsohon tsarin da matakan kubutar da rayuka da suke rage yawan mace-mace.
2 Yuli 2025

Daga Pauline Odhiambo

Abubuwa masu ban tsoro, matsanancin rashin jini da yawan kwanciya a asibiti na tsawon makonni a lokacin farkon juna biyunta, duk Aminata Coulibaly ba ta taɓa tunanin za ta samu kanta cikin wannan halin ba.

Yayin da take fama da cutar sikila, matar mai shekaru 28 ‘yar kasar Cote d'Ivoire ta san hatsarin da ke tattare da ita sosai lokacin da ta fahimci cewa tana da ciki.

"Na ji tsoron ba zan tsira na ga jaririna ba," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

Ba Aminata kadai ke cikin tsoro ba. Dubban matan da ke fama da cutar sikila a fadin Afirka da ma wajen nahiyar na shiga cikin bala'in rashin sanin ko za su tsira da cikin nasu.

Duba ga alkaluma a duniya baki daya, matan da ke fama da cutar sikila na fuskantar matsalar mace-macen haihuwa sau 4 zuwa 11 fiye da waɗanda ba su da ciki. Haka ma jariransu na cikin hatsarin mutuwar kafin haihuwa, ko su zo bakwaini, ko kuma rashin nauyi.

A ranar 19 ga watan Yuni, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar da ka'idojin farko na duniya don inganta kula da ciki ga mata kamar Aminata, suna masu bayar da shawarwarin da suka dogara kai shaida don tabbatar da haihuwa cikin aminci.

Yanayi mai hatsari

Kwayoyin cutar sikila na nan kamar wasu kwayoyin jini da ke da siffar jaririn wata da suke tohe jiyoyin jini, wanda ke janyo mummunan yanayin da ka iya kisa. Wadannan hatsari na yawaita a lokacin da ake dauke da juna biyu.

Cutar Sikila ta shafi kimanin mutane miliyan 7.7 a duniya baki daya inda kashe 80 suke a Afirka, kamar yadda sabbin ka’idojin suka bayyana.

Tuni aka yi watsi da matakan da ake bi don maganin cutar a baya, wadanda suke dogara kan matakan kasashe masu arziki sosai, da ba lallai su yi tasiri a kasashe matalauta ba.

“Sabbin tsare-tsare da ka’idojin na kawo sauyi matuka,” in ji Dr Pascale Allotey, daraktar kula da lafiyar mata masu ciki kuma mai bincike a WHO.

“Idan aka samu kulawa yadda ya kamata, mata masu juna biyu da ke da cutar sikila na iya zama lafiya. Amma muna bukatar zuba jari na gaggawa don samar da irin wadannan kula da lafiya a ko’’ina.”

Zabi mai karya zukata

A wajen mata da yawa, hatsarin na janyo daukar matakai marasa dadi.

“An fada min cewa samun yara na iya kashe ni,” Fatoumata Diallo, mace ‘yar Senegal da aka gano na dauke da cutar tun tana ‘yar karama ta shaida wa TRT Afrika.

“A lokacin da na yi aure, ni da mijina muka duba yiwuwar daukar hatsarin: Ko na rike cikina ko na zubar da shi kawai?”

Bayan tuntubar kwararru, ta haifi 'ya'ya biyu, ko da yake duka biyun na bukatar kulawar likitoci sosai.

"Na yi sa'a. Mata da yawa ba su da wannan zabin," in ji matar 'yar shekaru 32.

Sabbin ka’idojin na WHO na da manufar kula da cutar sikila yayin da ake dauke a juna biyu, tare da bayar da shawarwari da suka dace, ciki har da bayar da da folic acid da iron da ake bayarwa a tyabkubab da ke da cutar cizon sauro.

Kula da ciwo da ke da alaƙa da cutar sikila  wani babban al'amari ne mai muhimmanci.

Ka’idojin sun kuma fitar da matakan riga-kafi daga kamu wa da cututtuka da daskarewar jini, suna bayar da shawarar yadda za a yi ƙarin jini a cikin yanayi mai matukar hatsari, da kuma karfafa ingantaccen sa ido ga uwa da jariri a duk lokacin da take da juna biyu.

Kulawa ta musamman

Yayin da ka’idojin suka zama babban matakin cigaba, har yanzu ba a samun damar gudanar da bincike yadda ya kamata game da cutar ta sikila, musamman alamominta a lokacin da mace ke dauke da juna biyu. Kwararru na cewa ba a ware isassun kudade don yaki da cutar.

Yawancin maganin da ake ba su da bayanan aminci ga iyaye mata masu shirin haihuwa, waɗanda a tarihi aka cire su daga gwaje-gwajen asibiti.

"Wannan shi ne masomi," Dr Doris Chou, jami'in kula da lafiya na WHO kuma wanda a rubuta ka’idojin sabon shirin.

"Mata masu ciwon sikila na buƙatar tattaunawa da wuri, tattaunawa tare da masu kula da lafiyarsu don yanke shawara mafi kyau game da lafiyarsu da ta jariransu."

Waɗannan ka’idoji su ne na farko a cikin jerin ayyukan WHO na magance cututtukan da ba sa yaduwa a lokacin da suke da juna biyu, a yayinda rubuce-rubucen bincike na nan gaba da za a yi a nan gaba za su tabo ciwon sukari, yanayin lafiyar zuciya, da lafiyar kwakwalwa.

A yayin da cututtuka masu tsanani ke ƙara bayar da gudummawa ga mace-macen mata masu juna biyu, buƙatar daukar matakan da aka samar na bai daya na bayyane karara a gare mu. Ga miliyoyin mata masu ciwon sikila, waɗannan ka’idoji na iya nufin bambanci tsakanin rayuwa da mutuwa, da damar daukar 'ya'yansu a kafadunsu.

A lamarin Aminata, kulawa ta musamman a lokacin da take da ciki na biyu ya tabbatar da cewa ta haifi yarinyarta lafiya.

"Ina so duk macen da ke da ciwon sikila ta sani cewa haihuwa ba yanke hukuncin kisa ba ne," in ji ta. "Tare da kulawar da ta dace, za mu iya tsira kuma mu bunƙasa."

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us