NIJERIYA
2 minti karatu
Mutum 13 sun nutse a cikin kogi a lokacin da suke tsere wa 'yan bindiga a Zamfara
Lamarin ya faru ne a ranar Juma'a da tsakar rana inda 'yan bindiga suka kai hari kan ƙauyuka biyu a Birnin Magaji, mutanen sun rasu ne bayan kwale-kwalen da suke ciki ya kife sakamakon lodi ya yi masa yawa.
Mutum 13 sun nutse a cikin kogi a lokacin da suke tsere wa 'yan bindiga a Zamfara
Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin Nijeriya da ‘yan bindiga ke yawan kai hare-hare. / Getty
11 awanni baya

Akalla mutane 13 sun rasu sannan fiye da 20 sun ɓace a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Nijeriya bayan jirgin ruwan da suka hau don tsere wa harin wasu ‘yan bindiga ya kife a cikin kogi, kamar yadda mazauna yankin da jami’ai suka bayyana a ranar Asabar.

Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin Nijeriya da ‘yan bindiga ke yawan kai hare-hare.

Maharan sun kai hari kan ƙauyuka biyu a Birnin Magaji a ranar Juma’a da rana, lamarin da ya sa mazauna yankin suka tsere zuwa bakin kogin da ke kusa, inda jirgin ruwa guda daya kawai ya kasance, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

“Babban ɗana da wasu ‘yan uwa biyu sun kasance cikin mutane 13 da suka mutu lokacin da jirgin ya cika da mutane fiye da kima,” in ji Shehu Mohammed, wani ma’aikacin lafiya a Birnin Magaji, a tattaunawarsa da Reuters.

Maidamma Dankilo, hakimin Birnin Magaji, ya tabbatar da cewa mutane 13 daga cikin jirgin sun mutu, 22 an ceto su, yayin da 22 har yanzu ba a gano su ba.

A makon da ya gabata, ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane biyu kuma sun yi garkuwa da fiye da 100 a wani hari da suka kai kimanin kilomita 150 (mil 95) yamma da Birnin Magaji.

Zamfara ta samu rahotonni 50 na garkuwa da mutane a tsakanin watan Yulin 2024 zuwa Yuni 2025, inda aka sace mutane 1,064, kamar yadda wani rahoto daga cibiyar bincike ta SBM Intelligence da ke Legas ya bayyana a wannan makon.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us