Dakarun Tsaron Nijar FDS sun samu manyan nasarori a yaƙin da suke yi da kungiyoyin ta’addanci, inda suka gudanar da jerin manyan hare-hare daga 23 zuwa 28 ga watan Agusta a yammacin ƙasar.
A cewar rahoton mako-mako na FDS, waɗannan hare-haren da aka gudanar ƙarƙashin Operation Niya da Operation Almahaou sun daƙile harin kwanton-ɓauna da lalata bama-baman da aka dasa, da kuma tarwatsa cibiyar da ‘yan ta’addan ke ajiye kayayyakinsu
A ranar 23 ga Agusta, yayin sintiri tsakanin garuruwan Say da Tamou, dakarun sun gano bama-bamai guda uku da aka ɓoye a kusa da Illa Fari. Rundunar injiniyoyin soja ta yi gaggawar zuwa wurin inda suka lalata su cikin aminci, abin da ya ceci rayukan jama’a tare da bai wa dakarun damar ci gaba da aikin su cikin kwanciyar hankali.
Bayan kwana biyar, a ranar 28 ga Agusta, dakarun sun kaddamar da hari na musamman bisa bayanan sirri a yankin CFA Moussa, inda suka kai samame kan wata cibiyar ajiye kayayyakin ta’addanci. Dakarun sun kashe ‘yan ta’adda takwas a wannan samamen.
An kuma ƙwace bindigogin AK-47 guda biyu, babura da dama ciki har da babaru masu ƙafa uku guda biyu, da kuma man fetur da yawa da ake zargin an tanada ne domin tallafawa ƙungiyoyin da ke ɓoye a yankin.
Rahoton ya bayyana cewa wannan samame ya yi matuƙar illata hanyoyin da ‘yan ta’addan ke bi domin samun kayayyaki.
Operation Almahaou: An daƙile kwanton-ɓauna a Kandaji
A arewacin Tillabéri, ƙarƙashin Operation Almahaou, sojojin FDS sun sake nuna ƙwarin gwiwa. A ranar 27 ga Agusta, wasu ‘yan ta’adda sun yi ƙoƙarin kai harin kwanton-ɓauna a kan hanyar Kandaji zuwa Ayorou. Sai dai ankarar da sojoji cikin gaggawa suka yi ta yi sanadin daƙile harin rahotanni suka tabbatar babu wanda ya rasa ransa a cikin dakarun na Nijar.
Bayan haka, binciken da aka gudanar ya kai ga damƙe mutane huɗu da ake zargi da hannu a shirya wannan hari. An mika su ga hukumomin tsaro domin yi musu tambayoyi da tattara bayanan sirri.
Sojoji sun yaba da ƙwarewa
FDS ta jinjina wa ƙwarin gwiwa da ƙwarewar dakarunta, tana mai cewa waɗannan hare-haren sun raunana ‘yan ta’adda, sun hana su walwala, tare da dakile hanyar kayayyakin agajinsu a yammacin ƙasar.
Nijar na fama da hare-haren ‘yan ta’adda musamman masu iƙirarin jihadi, sai dai gwamnatin ta Nijar ɗin na cewa tana iyakar ƙoƙarinta wurin fatattakar su.