NIJERIYA
3 minti karatu
Yara ‘yan Najeriya 420,000 na fuskantar barazanar rashin abinci mai gina jiki a bana – UNICEF
Wakiliyar UNICEF a Nijeriya, Wafaa Elfadil Saeed Abdelatef ce ta yi wannan gargadin a lokacin ziyararta ofishin UNICEF na Maiduguri a ranar Alhamis.
Yara ‘yan Najeriya 420,000 na fuskantar barazanar rashin abinci mai gina jiki a bana – UNICEF
Nigeria na daga cikin ƙasashen da ke fama da ƙarancin abinci musamman a yankunan da ake fama da matsalar tsaro / AP
10 awanni baya

Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya gargadi cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, yara 420,000 na iya mutuwa daga cikin yara miliyan 3.5 da ke fama da matsanancin ƙarancin abinci mai gina jiki a Nijeriya.

Wakiliyar UNICEF a Nijeriya, Wafaa Elfadil Saeed Abdelatef ce ta yi wannan gargadin a lokacin ziyararta ofishin UNICEF na Maiduguri a ranar Alhamis, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

“Nijeriya na da yara miliyan 15 ‘yan ƙasa da shekara biyar da ke fama da ƙarancin abinci mai gina jiki, kuma yara miliyan 3.5 na cikin haɗarin kamuwa da matsanancin ƙarancin abinci mai gina jiki. Daga cikin waɗannan yara miliyan 3.5, yara 420,000 za su iya mutuwa a shekarar 2025 idan babu wani sauyi.


“Kashi 40 cikin ɗari na yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar na da matsalar rashin girma — wato rashin samun cikakken girman jiki da kuma yin wayau da wuri hankali idan ba a ɗauki mataki yanzu ba,” in ji ta.

Abdelatef ta ce sai an hanzarta samar da kuɗi da kayan abinci na cikin gida da kuma faɗaɗa cibiyoyin jinya, idan ba haka ba Nijeriya na iya rasa dubban ɗaruruwan yara ta hanyar yunwa, cututtukan da za a iya kauce musu, da kuma rashin kulawa.

Ta ƙara da cewa yankin Arewa maso Gabas na ci gaba da fama da rikicin jinƙai inda mutane fiye da miliyan 4.5 ke cikin matsananciyar buƙatar tallafi.

A game da ilimi kuma, Abdelatef ta jaddada cewa Nijeriya na da matsaloli ta wannan ɓangaren sosai, inda yara miliyan 18.3 ba sa zuwa makaranta—miliyan 10.2 daga cikinsu yara ne masu shekarun firamare, yayin da miliyan 8.1 ke da shekarun ƙaramar sakandare.

 “Wannan kusan ɗaya cikin uku na yaran Nijeriya ne. Kowace shekara, yara miliyan 3.9 ba sa kammala makarantar firamare, sannan miliyan 4.2 ba sa kammala ƙaramar sakandare.
“Kashi 27 cikin ɗari kacal na yara masu shekaru 7 zuwa 14 ne ke iya karantawa da fahimta, sannan kashi 75 cikin ɗari ba sa iya warware ƙananan lissafi. Matsalar ilimi tana da nasaba da samun damar zuwa makaranta da kuma ingancin karatu.

A ɓangaren rigakafi da kuma tsirar yara, Abdelatef ta bayyana cewa Nijeriya na da yara fiye da miliyan 2.1 da ba a taɓa yi wa rigakafi ko ɗaya ba, adadin da ya fi kowace ƙasa a duniya.

“Kusan ɗaya cikin uku na yara ‘yan shekara ɗaya ba su taɓa karɓar kowace allurar rigakafi ba, lamarin da ke barinsu cikin haɗarin kamuwa da munanan annoba da za a iya kauce musu kamar ƙyanda da diphtheria da sanƙarau da kuma nau’ukan cutar shan inna da ke yawo,” in ji ta.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us