KASUWANCI
2 minti karatu
Gwamnatin Nijeriya ta amince da tsarin sayar da danyen manta a farashin Naira
Majalisar Zartarwar Tarayyar Nijeriya ta amince da ƙaddamar da tsarin da ta dakatar a baya, na sayar da ɗanyan manta a farashin Naira ga matatun man da ke cikin ƙasar.
Gwamnatin Nijeriya ta amince da tsarin sayar da danyen manta a farashin Naira
/ Reuters
9 Afrilu 2025

Ma’aikatar Harkokin Kuɗi ta Nijeriya ta bayyana cewa gwamnatin ƙasar ta amince da komawa kan tsarin sayar da man da ake haƙowa a ƙasar bisa farashin Naira ga matatun man ƙasar.

A Larabar nan ne ma’aikatar ta fitar da wannan sanarwa a shafinta na X wanda ya fayyace makomar shirin da aka dakatar a baya.

Tsarin da ya ƙare ranar 31 ga Maris ɗin shekarar nan, ya yi aiki na tsawon watanni shida wanda ya ƙunshi yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya, da kamfanin mai na ƙasar, NNPCL.

Kafin a cigaba da tsarin, matatar man Dangote da jingine tsarinta na sayar da albarkatun mai a farashin naira, inda ta ɗora alhakin hakan da dakatar da shirin gwamnati.

Kwamitin shiri

Kwamitin da ke aikin daidaita tsarin kasuwancin mai a Nijeriya ya tabbatar da cewa a yanzu wannan tsari ba na wucin-gadi ba ne, mai dogon zango ne kuma yana da ƙudurin taimaka wa Nijeriya rage dogaro kan kuɗaɗen ƙasashen waje.

A ranar Talata ne kwamitin ya cim ma matsya bayan yin bitar cigaban da aka samu wajen magance matsalolin da harkar mai ke fusknata a ƙasar.

Haka nan kwamitin ya jaddada ƙudurin gwamnatin Nijeriya na aiwatar da tsarin da ya samu goyon bayan majalisar zartarwar ƙasar.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us