Liverpool ta amince da sayar da Nunez ga Al Hilal ta Saudiyya kan rangwamen farashin fam miliyan 56.6.
A ƙarshe dai ɗan wasan Liverpool Darwin Nunez zai bar ƙungiyar bayan kwashe shekaru uku a can.
Tun zuwansa Liverpool a 2022, ɗan wasan ɗan asalin Uruguay ya ci jimillar ƙwallaye 40 a wasanni 143.
A kakar bara ƙarƙashin sabon koci Arne Slot, tagomashin Nunez ya ci ƙwallaye bakwai ne kacal.
Sai dai farashin da Al Hilal ta saye shi yanzu na nufin Liverpool ta yi faɗuwar miliyoyin kuɗi saboda ta sayo shi ne kan £64m da ɗoriya.
A yanzu rahotanni na cewa Al Hilal za ta biya ƙayyadajjen farashin fam miliyan 46.2 da ƙarin da zai kai jimillar kuɗin zuwa fam miliyan 56.6.
A baya AC Milan ta Italiya ta yi tayin sayan Darwin Nunez, amma da wuya su iya ba da farashin da ya kai wannan adadin na Al Hilal.